wa nene ya cancanci bauta shi kadai  ?


Da sunan Allah mai rahama, mai jin kai

wa nene ya cancanci bauta shi kadai  ?

 

Wannan kauni mai fadi, da wannan dabi' mai kayatarwa, da wannan mutun wanda aka kyautata halittarsa, wanda aka baiwa hankali da iyawa mai bada mamaki, da dukkan halittu masu rai da wadanda ma ba su da rai; wadanda duka suke tafiya akan tsari mai kayatarwa da bada mamaki …

Dukkan wadannan ababen da suka gabata suna tabbatar mana cewa akwai wani mahalicci wanda ya samarda su, wanda yake mai karfin iko ne, ma wadaci, mai tafiyar da al – amurra da hikma da iyawa, da kuma adalci.

Wannan mahaliccin shine Allah, ubangijin kowa, da komi.

Wa nene "ALLAH"?

Shin shi daya ya ke ? ko kuma su da yawa ne ?

Wannan tambayoyi ne da za mu gabatar ga wannan kaunin mai tafiya a bisa tsari mai ban mamaki.

To, sai mu tsaya mu saurari amsar, mu kuma yi tunani mai kyau.

Ga amsar da shi wannan kaunin yake bamu:

Shin ba ku ganin kyawon ababen da ke ciki na? Shin tsarin da suke tafiya a kai ba ya  kayatarda ku?

Shin ba ku al ajabi game da tsarin wannan rayuwar?

Mi nene ra' ayin ku da ka ce: akwai fiye da mahalicci guda?

Shin za' a samu wannan tsari mai kayatarwa?

Ba ku ganin cewa inda ba shi kadai ne ba za' a samu sabani tsakaninsu? Wanda kuma sakamkon hakan dukkan wannan tsarin za' a rasa shi ? saboda ko wane daya daga cikin su zayi kokarin zartar da na shi tsari ne.

Inda ba shi kadai yake ba abin da zai faru shine:

Ko dai karfin su yazo daidai, sai ya kasance babu wanda zai iya zartar da wani abu akan kotankocin shi. To ina za' a taba yin abin bauta mai rauni?

Idan ba haka ba, dayan su zai samu rinjaye akan sauran, kenan sai ya kasance shi ne mahaliccin su wanda ke cacantar a bauta masa shi kadai.

ALLAh ya na cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

« Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu ( sama da ƙasa ) fãce Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al'arshi daga abin da suke siffantãwa ».

ALLAh ya na cewa a cikin  al kura' ni mai tsarki:

« kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne ( akwai abin bautawa tare da Shi ) , lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa ». [Suratul Al-Mu'minun 91].

Dan haka wannan kaunin da dukkan abin da ke cikin shi yana nunine zuwa gare mu cewa wanda ya samar da shi, shine guda  da ba shi da abokin tarayya.

To, wane ne Allannan guda?

 

 

Lalle wajibi ne akan wanda ke kiran wanin ALLAH ya kawo hujjoji dake nuna cewa ya cancanci a bauta mishi.

ALLAh yana cewa a cikin  al kura' ni mai girma: {wadannan muta' nen namu da suka riki waninsa [ALLAH] abin bautawa, mi ya sa basu kawo wata hujja bayyananna akan cancantar a bauta musa? To, wanene mafi zaluuci fiye da wanda ya kagi karya ga ALLAH}.

Shin wannan abin bautar wuta ce?!

Shin mutun zai hada makamashi , ya kunna wuta , ya kuma tsare wutar nan kar iska ko ruwa ya kashe wannan wutar, ko ya rage karfinta, sa' annan ya komo ya kaskantar da kansa ga wannan wutar da ya hada kuma ya tsare ?!!!!

Shin hankali zai iya yarda cewa wannan wutar ta zamanto ita ce abin bauta wadda ake neman taimakonta wajen kauda zalunci da abin da yayi kama da haka?

ALLAh ya na cewa a cikin  al kura' ni mai girma: {wadannan da kuke kira koma bayansa basu iya taimaka muku, basu iya ma taimakon ka' nunsu}.

Ko shi Allan nan gunki ne na katako, ko dutsi wanda mutun ya sassaka da kansa?

Gunki baya ji, baya gani, baya Magana, baya motsi, baya anfani, baya tsutarwa!

ALLAh ya na cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

« Kuma inã rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga gumãkanku a bãyan kun jũya kunã mãsu bãyar da bãya.

Sai ya sanya su guntu- guntu fãce wani babba gare su, tsammãninsũ sunã Kõmãwa zuwa gare shi.

Suka ce: Wane ne ya aikata wannan ga gumãkanmu? Lalle shĩ, hakĩka, yanã daga azzãlumai.

Suka ce: Mun ji wani saurayi yanã ambatar su. Anã ce masa Ibrahĩm.

Suka ce: To, ku zo da shi a kan idanun mutãne, tsammãnin su zã su bãyar da shaida.

Suka ce: Shin kai ne ka aikata wannan ga gumãkanmu? Yã Ibrahĩm!

Ya ce: Ã'a, babbansu, wannan, shĩ ya aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance sunã yin magana.

Sai suka kõma wa jũnansu suka ce: « Lalle ne kũ, kũ ne azzãlumai.

Sa'an nan kuma aka sunkuyar da su a kan kãwunansu ( sukace, ) Lalle, hakĩka, kã sani wadannan bã su yin magana.

Ya ce: Shin to, kunã bautã wa abin da, bã ya, amfãnin ku da Kõme kuma bã ya cũtar da ku baicin Allah?

Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, baicin Allah! Shin to, bã ku hankalta?»   [Suratul Al-Anbiya 57 - 67].

-Abin al- ajabi, abin da larabãwa suka kasance suna aikatawa: domin daya da ga cikin su yana mai balaguro da abin bautarsa wanda ya yi da gumbar dabino, idan ya ji yunwa sai ya cinye wannan abin bautar nashi!

Idan kwa abin bautar nashi na dutsi ne sai ya maida shi murfu abin dafa abinci akai! Ba yan ya koshi sai ya dauki ubangijin nan nashi, ya ci gaba da mishi ruku' u da sujada!!!

Shin hankali zai iya yarda da cewa gunki abin bauta ne?

ALLAh yana cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

« Suka ce: Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su. 
Ya ce: Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira? 
Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku? »  [Suratul Al-Shu'ara 71 -73].

- ko kuma abin bautar nan zai kasance rana ko daya daga cikin tauraru wadanda suke masu gushewa, masu tafiya a kan tsari na musamman , wadanda basu da iko game da canza matafiyar su? Yaya wanda ba ya iya tafiyar da al – amurran shi zai kasance ya mallaki anfani da cutarwa ga dan adam?

ALLAh ya na cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

« Na sãme ta ita da mutãnenta, sunã yin sujada ga rãnã, baicin Allah, kuma Shaiɗan ya ƙawãtã musu ayyukansu, sabõda haka ya karkatar da su daga hanya, sa'an nan sũ, ba su shiryuwa. 
Ga su yi sujada ga Allah Wanda Yake fitar da abin da yake a ɓõye, a cikin sammai da ƙasa, kuma Yã san abin da kuke ɓõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa ».

- Ko kuma mutun ne abin bautar tasu?

Shin tare da kyawon shi, da karfin shi, da hankalin shi, da wadatar shi, yana  iya kare kanshi daga rishin lafiya, ko kuma ya dawwamarda kan shi a duniya ba tare da ya mutu ba ?

ALLAh yana cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

« Shin, ba kayi dubi ba zuwa ga wannan da ya yi hujjatayya da Ibrãhĩm a cikin ( al'amarin ) Ubangijinsa ba  dõmin Allah Yã bã shi mulki, a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: Ubangijina Shi ne Wanda Yake rãyawa, kuma Yana matarwa. Ya ce: « Nĩ ina rãyarwa kuma ina matarwa. Ibrãhĩm ya ce: To, lalle ne Allah Yana zuwa da rana daga gabas: To, ka zo da ita daga yamma. Sai aka ɗimautar da wanda yakãfirta. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne azzãlumai ».

Wasu daga cikin mutane, idan hankalin  wasu mutune ya basu mamaki sai su dauke su abin bauta. Sun manta cewa mutun yana tare da rauni a ko wane lokaci, ikonshi kuma takaitacce ne, ba ya iya kewayo ga abin da ke kewaye da shi.

Misalin sa kamar mutun ne wanda sarki ya tsare shi a gida, sai ya buda mishi wasu kananan kofofi; kofa a gabas mai zuwa ga kogi, guda kuma a yamma mai zuwa ga dutsi, guda kuma a arewa tana zuwa ga fadar sarki, guda kuma a kudu tana zuwa ga gurin wasa.

Wannan wanda aka tsare shine hankali ko rai, wannan gida kwa shine gangar jiki, wannan kofofi  kwa sune bangarori na mutun wanda ya ke riskar al – amurra da su: ido yana kula da abin da ya shafi kamanni, bangren kunne ya na kula da abin da ya shafi sauti, harshe yana kula da abin da ya shafi dandano, hanci yana kula da abin shaka, fata tana kula da abin da ya shafi abin tabawa.

Abin tambaya shine: shin ko wane gaba ya na riskar dukkan bangaren da yake kula da shi ?

Wannan wanda aka tsare ba dukkan kogin nan yak e gani ba ta wannan kofar da aka buda mishi, haka ma ido ba ya ganin kome da kome.

Ba ma ganin kwayoyin tsuta da ke cikin kwanon ruwa tare da cewa akwai milyoyin kwayoyin tsutar a ciki.

Dan haka bangarorin jikin mu suna riskar wasu da ga cikin ababen da suke iya riska ne, ba duka ba.

To, yaya za mu riki wannan takaitaccen hankalin ubangijin mu?

 

Ko kuma ubangiji shine daya daga cikin ababe da yawa wadanda wasu su ke bautawa, ba tare da sun kawo hujja ba a kan kasancewar su sun cancanci bauta ba?

ALLAh ya na cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

« Allah ne Wanda Ya halitta ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rãyar da ku. Ashe, daga cikin abũbuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga wadannan ahũbuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya daukaka bisa ga abin da suke yi na shirki ».

Dukkan ababen da suka gabata da wasu suke riko abin bauta, babu wani wanda zai iya kawo hujja akan cewa suna iya halittar wani abu a cikin sammai ko cikin doron kasa.

ALLAh ( ma daukaki )  ya na cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

« Kuma suka riki abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa ». [ Suratul Al-Furqan ]

Kaka hankali zai yarda ya girmama abin da ya kera da hannun sa ? Ko kuma abin da baya mallakar anfani ko kore cuta ga kansa ? Kaka yake neman wani anfani da ga mai wannan sifofi ? kaka yake tsoron tsutarwa daga wanda bai wadatar da kanshi ba?

ALLAh ( ma daukaki )  ya na cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

« Ka ce: Ashe kunã bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta sabõda ku kuma haka wani amfani alhãli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani ? ».

Lalle wannan kaunin mai girma yana nuni ga girman mahaliccin sa ne, ya na kuma goda muma cewa mahaliccin sa shi kadai yake, ba shi da abokin tarayya.

Shin zai yuwu ALLah ya kasance dayan uku kamar yanda nasarawa ke fada? Ma'aifi ( Allah ), da da ( Isa ), da ran tsarki.

Wasu a cikin su suna da akidar cewa Maryam ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare ta ) ma allah ce.

Wajen su ALLAH daya ne a cikin uku, kuma uku ne a cikin daya ( tsarki ya tabbata ga ALLAH da ga wannan mummunar maganar ).

Shin zai kyautu ga mahalicci, mai daukaka, mai karfi da iko, mai kowa, mai kome, ya kasance a cikin ma' aifar wata mace, yana mai jujjuyawa a cikin kazamta da duhun ma' aifa wani lokaci, bayan haka ya zo cikin wannan rayuwar yana jinjiri mai bukatar a kula da shi wajen shayarda shi da abin da yayi kama da haka har ya girma… yana mai kuka da bukatar a tsabtace shi a kuma yi lallashin shi, yana mai bayan gida da futsari bayan ci da sha da  barci ?!!!! bayan haka kuma a mishi sallatu , ya kuma shigo garin kudus yana mai shekaru goma sha biyu, dan ya yi karatu tare da yaran yahudawa, ya kuma tambayi malaman yahudawa ababen da ke kamata ga mutun?!!!!

Bayan haka yahudawa su kasance suna korar shi, yana mai gudu daga wannan gurin zuwa wani, har yayin da suka samu cabke shi, suka gana mishi azaba da wulakanci iri iri; suka sa mishi hular kaya, sa' an nan suka kaishi suka tsire shi ga itatuwa biyu da aka saba, tare da cewa yana neman su masa rahama, su kuma ji kan sa ?!!!!

Kaka haka zai abku ga mahaliccin sammai da kassai?

Kaka haka zai kasance ga mai rayarwa da kashewa, mai karfi, mabuwayi?

Suna cewa hikmar sa ita ce ta son yabar makiyan sa su yi hakan da shi, domin su cancanci azaba mai tsanani a wutar jahim, domin kuma ya fanshi annabawa da manzanni da waliyyai da ran Shi, ya fitar da su daga kurkukun iblis!

To, kaka Isa ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) zai dauki laifukan dukkan 'yan adam tare da cewa yazo a cikin "at taura  wadda dukkan nasara ke tsarkakewa kamar yanda yahudawa ke tsarkake ta:

 

« ba' a kashe iyaye da laifin 'ya'ya, haka ma ba' a kashe 'ya'ya da laifin iyaye; kowa ana kashe shi da laifin sa ne ».

Wannan nassi ne wanda ke nuni a bayyane cewa kowa yana daukar nauyin aikin sa ne.

To, yaya mutuwar Isa ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) za ta kasance fansar zunubban dukkan masu zunubi da barna?

Sa' an nan Isa ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) ya rasu, aka binne shi a cikin kasa, bayan haka ya tashi, ya je saman al – arshin Shi, ya dauki mulkin Shi da matsayin Shi na ubangiji bayan dukkan ababen da suka gabata !!!

Suna fadar haka tare da cewa da yawa da ga cikin nasara na farko sun tafi akan cewa isa ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) ba' a kasha Shi ba, ba' a kuma soke Shi ba.

Abin mamaki ne fadar nasara cewa isa ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) Allah ne tare da cewa isa da kan shi yana kafa hujja da nassosin "at – taura" akan cewa ALLAH shi kadai yake ba shi ma kamanci!

Daga cikin nassosin "at' – taura" akwai maganar ash' iya'u: « hakika kai ne Allah wanda ke a boye, ya ubangijin isra' ila mai ikhlasi ».

Haka ma Isa  ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) ya ce da su ya na mai tabbatar da kadaitar ALLAH da kasancewar shima mai bauta ne ga Shi Allan: « ALLAH shine ya sanya ni manzo, al masihu, ni bawon Shi ne, ni ina bautawa Allah ne wanda yake shi kadai, saboda ranar kubutarwa ».

Idan ALLAH ya kasance ba' a ganin Shi, kaka Isa zai kasance shi ne Allah, al hali kwa yana tare da su?

Dan haka suna karya ne ga Isa ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ), wanda ke tabbatar da cewa shima bawon Allah ne, yana mai bayyana haka yayain da yake cewa: « lalle Allah ne ubangiji na, ni da ku gaba daya, kuma shine ya cancanci ni da ku duka mu bautawa ».

Kuma yana bayyana  musu cewa shi manzon Allah ne zuwa gare su kamar yanda aka aiko mazonni gabanin shi; kamar yanda yazo a cikin linjila  (yuhanna) yayin da yake adu' a: «lalle rayuwar ka wada ke mai wanzuwa tana wajabtawa mutane su shaida cewa kai ne ALLAH na gaske, wanda ke shi kadai, su kuma shaida cewa kai ne ka aiko Isa al masihu ».

Ya kuma ce da bani isra' ila: «kuna son kashe ni, ni kwa mutun ne da ke gaya muku gaskiya da naji Allah ya fada ».

Lalle halittar Isa ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) daga uwa ba tare da uba ba ta kasance aya mai girma da ke nuni ga girman wanda ya halicce shi, wanda ya halicci Adam ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) ba tare da uwa ba ko uba, ya kuma halicci hawwa ba tare da uwa ba, ya kuma halicci sauran halitta daga uwa da uba.

A yoyi  kwa da ya baiwa Isa( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi )  kamar rayar da matacce, lalle wannan ya kasance da iznin Allah ne, kamar yanda Isa ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) da kan shi ya tabbatar musu a cikin adu' ar sa, yayin da ya ce: «ni ina mai godiya da yabo gare ka a wannan, da dukkan lokaci, ina rokon Ka ka rayar da wannan mataccen; saboda bani isra' ila su san cewa kai ne ka aiko Ni, kuma kana karban rokona ».

Ya kuma zo a cikin injila ta( mattah ) fadar shi gare su: «kar ku kirayi wani "uba" a doron kasa, "uban ku" guda ne, Ya na sama, kar kuma ku kirayi wani malami, domin malamin ku shine Al masihu, shi kadai ».

"uba" a maganar su shine wanda ke tattalin wanin shi; abin nifi: kad ku ce ubangijinku da  abin bautar ku yana nan kasa, domin shi yana sama ne. sa' an nan ya ajie kanshi a matsayin da Allah ya ajie shi, shine ya karantar da mutane cewa Allah da ke sama kadai ne abin bautar su.

Allah ya bamu labarin mahawarar da za ta kasance tsakanin shi da Isa dan Maryam ( tsira da rahamar ubangiji su karu gare shi ) ranar lahira, sai ya ce:

« Kuma a lõkacin da Allah Ya ce:   Yã Ĩsã dan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, 'Ku rike ni, ni da uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?   ( Ĩsã ) Ya ce: « Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a gare ni, in fadi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã fade shi, to lalle Ka san shi, Kanã sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin abubuwan fake ne. 
Ban fada musu ba fãce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nã kasance mai shaida a kansu matukar nã dawwama a cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karbi raina   Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan dukkan kõme, Halartacce ne.  
Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bãyinKa ne, kuma idan Ka gãfarta musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima. »  [Suratul Al-Ma'idah 116 – 118].

Gabanin nasara yahudawa sun ce uzairu dan Allah ne, kamar yanda mushrikan larabawa – gabanin nasara – suka ce: mal' iku diyan Allah ne.

Hakika sifanta Shi  Allah da cewa yana da da, wannan suka ne gare Shi da tauyewa daga sifofin Shi na kama' la ( mahalicci ) ( mai cikekken  mulki ) ( mai juya kome da kowa ); lalle Allah ba shi da da, saboda babu nakasa ta bukata ko wata daban ma tare da shi, shi mawadaci ne daga wanin shi, bashi kuma da kotankoci.

Inda ya riki da, da dannan zai zama kotankocin  shi, inda yana da da, da ya kasance ma bukaci zuwa ga taimakon dan nan, da kuma zai kasance yana da nakasa.

Shin yanzu ka san wanene Allah ?

Dukkan wanin Allah abin halitta ne, mullaka ne na Allah, yana juya shi yanda yake so, babu kuma wanda ke tarayya da Shi a cikin mulkin shi kamar yanda yake fada a cikin al – kura' ni mai tsarki:

« Ka ce: Ku kirãyi wadanda kuka riya ( cẽwa abũbuwan bautãwa ne ) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu ( sammai da ƙasa ) , kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su ».

Haka kuma babu tarayya da Allah a cikin halittarsa da mulkinsa da juya al – amurransa kamar yanda yake fada a cikin al – kura' ni mai girma:

« kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu ».

Haka kuma babu wani da ya taimaka mishi a cikin sammai da ƙasa kamar yake fada a cikin al – kura' ni:

« kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su ».

Kafin ƙarshe sai mu tsaya mu yi tunani game da amsar mutunen da ya gane hanyar Allah, da kuma hanyar wanda ya miƙa wiyan shi ga wadanda suka kuskure hanya, suka kuma yi taurin kai.

ALLAh ( ma daukaki )  ya na cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

Kuma mutãnensa suka yi musu da shi. Ya ce: « Shin kunã musu da ni a cikin sha'anin Allah, alhãli kuwa Yã shiryai da ni? Kuma bã ni tsõron abin da kuke yin shirki da shi, fãce idan Ubangijina Yã so wani abu. Ubangijina Ya yalwaci dukkan kõme da ilmi. Shin, ba zã ku yi tunãni ba? » 
81. « Kuma yãyã nake jin tsõron abin da kuka yi shirki da shi, kuma ba ku tsõron cẽwa lalle ne kũ, kun yi shirki da Allah, abin da ( Allah ) bai saukar da wata hujja ba game da shi? To, wane bangare daga sãshen biyu ne mafi cancanta da aminci, idan kun kasance kunã sani? »

« Wadanda suka yi ĩmãni, kuma ba su gauraya ĩmãninsu da zãlunci ba, wadannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu ».

Ka gane wanene ya ke cacantar a kiraye shi da sunan ALLAH, da kuma sifanta shi da abin bauta?

ALLAh ( ma daukaki )  yana cewa a cikin  al kura' ni mai girma:

« Allah ne wanda Ya halitta sammai da kasa da abin da yake a tsakãninsu a cikin kwãnuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Bã ku da, baicin Shi, wani majibinci kuma babu wani maceci. Shin, bã zã ku yi tunãni ba ? ». [Suratus sajdah 4 ].

« Ka ce: Wãne ne Ubangijin sammai da kasa? » Ka ce: Allah. Ka ce: « Ashe fa, kun riki wadansu masõya baicin Shi, wadanda ba su mallaka wa kansu wani amfãni ba kuma haka bã su tũre wata cũta? » Ka ce: « Shin makãho da mai gani sunã daidaita? Kõ shin duhu da haske sunã daidaita? ko sun sanya ga Allah wadansu abõkan tãrayya wadanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da jũna a gare su? » Ka ce: « Allah ne Mai halitta kõme kuma Shĩ ne Madaukaki, Marinjãyi ». [Suratul Al-Ra'd 16 ].

Da mun kasance mun san wanene Allah tare da hujjohi da dalilai bayyanannu.

Wannan kuma yana bayyana idan mu kayi tuna ni a cikin yanda ALLAH ya sifanta kan shi a cikin al kura' ni mai girma:

« Ka ce: Shi ne Allah Makaɗaĩci. 
Allah wanda ake nufin Sa da buɗata. 
Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba. 
Kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gare Shi ». [ suratul Ikhlãṣ ].

« Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma ».

« Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme ».

« Allah Shi ne wanda Ya ɗaukaka sammai, bã da ginshiƙai ba waɗanda kuke ganin su. Sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, kuma Ya hõre rãnã da watã, kõwane yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. Yanã shirya al'amari, Yanã rarrabe ãyõyi daki- daki, mai yiwuwa ne ku yi yaƙĩni da haɗuwa da Ubangijinku ».

« Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma ( Shi ) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai, wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku? 
96. Mai tsãgẽwar sãfiya, kuma Ya sanya dare mai natsuwa, kuma da rãna da watã a bisa lissãfi. vwannan ne ƙaddarãwar Mabuwãyi Masani. 
97. Kuma Shi ne Ya sanya muku taurãri dõmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da ruwa. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki- daki, ga mutãne waɗanda suke sani. 
98. Kuma Shi ne Ya ƙãga halittarku daga rai guda, sa'an nan da mai tabbata da wanda ake ajẽwa. Lalle ne Mun bayyanã ãyõyi daki- daki, ga mutãne waɗanda suke fahimta. 
99. Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa'an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi ( kõren ) ,  kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje- dumbuje makusanta, kuma ( Muka fitar ) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'ya'yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni. 
100. Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa ( Shi ) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa. 
101. Mafarin  halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne?

102. Wancan ne Allah Ubangijinku. Bãbu wani abin bautãwa fãce Shĩ, Mahaliccin dukan kõme. Sabõda haka ku bauta Masa kuma Shi ne wakĩli a kan dukan, kõme. 
103. Gannai bã su iya riskuwarSa, kuma Shĩ Yanã riskuwar gannai, kuma Shĩ ne Mai tausasãwa,Masani. 
104. Lalle ne abũbuwan lũra sun je muku daga Ubangijinku, to, wanda ya kula, to, dõmin kansa, kuma wanda ya makanta, to, laifi yanã a kansa, kuma nĩ, a kanku, bã mai tsaro ba ne. ».

A ƙarshe:

Kayi tunani game da wannan ayar ta cikin Al- kura' ni mai girma, wadda ke sanarda kai mi wanene Allah ta hanyar ni' imomin shi akan bayin shi:

« Ka ce: Godiya ta tabbata ga A1lah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa, waɗanda Ya zãɓa. Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi? 
Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa ( Allah da wani ) . 
Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba. 
Kõ wãne ne yake karɓã , kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni. 
Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku,kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi.

 

Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita,kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: « Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya. » 
Ka ce: « Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su.

 

Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne  ».  [Suratul Al-Naml 59 -65 ].