Tsarin gado a muslunci


Tsarin gado a muslunci

 

Raddi a kan wasu shubuhohi da ake yadawa game da Tsarin gado a muslunci

 

Wasu suna son su kawo rudani game da yanda muslunci ya raba gado, wannan kwa badan kome ne ba face son kawo suka ga wannan addinin da wannan shari'a; saboda sanya shakku a cikin zukatan musulmi da kuma raunana imanin su.

Yana daga cikin ababen da suke suka - a gaba gaba - yanda muslunci ya fifita kason namiji akan na mace a cikin gado. Suna cewa muslunci ya zalunci mace yayin da ya bata rabin kason namiji. Suna ganin cewa adalci shine abata kaso daidai da namiji.

Amsa ga wannan shubuha ita ce:

 

A dunkule-

 

Na farko: shi dai musulmi mutun ne mai imani da Allah da manzon sa; dan haka imaninsa ya kunshi yarda da shari'ar Allah da zuciyarsa, tare da samun natsuwa akan hakan; saboda ya san cewa Allah mai sanya kome a bagiren da ya kamata ne, kuma Shi mai yin kome da hikma da maslaha ne; domin Shine mai hikma gaba daya.

Yana kuma daga hikmar nan hukunce hukuncen raba gado, musulmi yana yarda da haka, kuma yana karbar shi da hannu biyu, ko da kwa hikmar ba ta bayyana gare shi ba.

Allah ( ma daukaki ) Yana cewa: «36. Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lõkacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zãɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, to, yã ɓace, ɓacẽwa bayyananna ». ] Suratul Al-Ahzab [.

Allah ( ma daukaki)  Yana kuma cewa: «51. Maganar mũminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa dõmin Ya yi hukunci a tsakãninsu takan kasance kawai su ce: Mun ji, kuma mun yi ɗã'ã, Kuma waɗannan sũ ne mãsu cin nasara. » ] Suratul Al- Nur [.

Amma tare da abinda ya gabata zamu iya neman sanin hikma a game da wannan hukunci domin mu kara yin imani, mu kuma samu karuwar natsuwa. Zai kuma kasance tare da haka raddi ga wadanda ke son ya bata sunan muslunci, tare da aikata rishin ladabi ga ubangijinsa; yayin da yake da'awar sani fiye da Allah madaukaki, yake da'awar cewa rabonsa ya fi na Allah!

Abu na biyu: lalle muslunci ya ba mace hakkinta, ya sanya mata wani kaso a cikin dukiya ta gado; yayin da ya kasance a can baya ba' a bata kome. Misali a jahiliya ba' a bata kome domin ita ba ta zuwa yaki, kuma ba ta nemo dukiya, sai Allah Ya bata wannan hukunci nasu daga tushe shi, Ya baiwa mace hakkinta Yana mai cewa: « 7. Maza suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mãtã suna da rabo daga abin da iyãye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi kõ kuwa ya yi yawa, rabo yankakke. »  ] Suratul Al-Nisa [.

Hasali ma mutan jahiliya sun kasance suna sanya mace cikin dukiya da ake gado; babban da na mamaci, ko kwa 'yan uwansa su suke da hakki na daukar ta a cikin gado, ko kuma su aurar da ita tare da amsar sadakinta; sai Allah ( ma daukaki ) Ya hana hakan a cikin fadarSa: « 19. Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su » ] Suratul Al-Nisa [.

Abu na uku: muslunci bai fifita namiji a kan mace a ko wane hali ba, hasali ma ya sanya kason mace a wasu halaye fiye da kason namiji.

Za mu iya kasa mas'aloli da aka fifita wani jinsi a kan wani zuwa kashi hudu:

Kashi na farko: kason namiji ya fi na mace; kamar idan sun kasance 'yan uwa maza da mata sai ya kasance mace tana da rabin kason namiji.

Kashi na biyu: kason ta ya yi daidai da na namiji; kamar idan sun kasance 'yan uwa (na gefen uwa), kuma kamar yanda yake a cikin gadon ma'aifi tare da ma'aifiya; ko wane daya daga cikin su yana da sudusi, idan ya kasance mamaci yana da reshe (da , ko dan da, koda sun sauka …) kamar yanda yake a cikin fadar Allah ( ma daukaki ): « Kuma iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi » ] Suratul Al-Nisa 11 [.

Kashi na uku: mace ta samu kaso fiye da na namiji; wannan kwa a halaye sun fi goma; kamar a fadar Allah ( ma daukaki ): « Idan sun kasance mãtã ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce ( kawai ) to, tana da rabi. Kuma iyãyensa biyu kõwane ɗaya daga cikinsu yanã da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani rẽshe ya kasance gare shi » ] Suratul Al-Nisa 11 [, uba namiji ne, yana daukar sudusi tare da cewa yana kasa da kason mace babu shakka; domin diya idan ta kasance ita kadai za ta dauki rabin dukiya, idan kuma sun kasance su biyu mata diyan mamaci; ko wace daya daga cikinsu za ta samu sulusi ( kashi daya a cikin uku ). A cikin dukkan wadannan halaye kason mace ya fi na namiji.

Kashi na fudu: mace ta samu gado tare da cewa wasu maza ma su gado ba su samu ba. Misali idan mutun ya mutu ya bar da, da diya, da 'yan uwa maza shakikai biyu ko fiye da haka; a wannan hali diyar nan da dan uwanta kadai za su gaji wannan dukiya: ita tana da kaso guda, shi yana da biyu, su kwa shakikai ba su da kome; saboda dan nan namiji ya kore su.

Dan haka fifita namiji a kan mace ba a ko wane hali ne ba.

B amsa a bayyane-

 

Na farko: fifita namiji akan mace a cikin rabon gado babu cin hakkin mace a cikinsa, saboda shari'a ba ta dau wani abu na mace ta bauwa namiji ba, hasali ma shi kyauta ce ta Allah ga magada; kuma Ya ba kowa abinda yake cancanta. Manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) Yana cewa: (lalle Allah Ya baiwa ko wane mai hakki hakkinsa).

Abu na biyu: a cikin fifita kason namiji akwai kyaye al amurra masu yawa: Namiji an dora masa nauyi wanda ba' a dora wa mace ba; kamar ciyar da iyali komin arzikinta, Allah ( madaukaki ) Yana cewa: « 34. Maza mãsu tsayuwa ne a kan mãtã, sabõda abin da Allah Ya fifita sãshensu da shi a kan sãshe kuma sabõda abin da suka ciyar daga dũkiyõyinsu. »  (  suratul Al-Nisa ).

1 - Kuma shi namiji yana daukar nauyi na ciyar da dukiya fiye da mace; misali biyan diya madadin wanda yayi kisa da kuskure, kuma yana daukar nauyin kaffara da suka shafi matarsa a cikin maganar malamai mai karfi; dukiyar namiji hanyoyin kashe ta suna da yawa fiye da na dukiyar mace; dan haka la'akari da hakan abu ne mai muhimmanci, kuma a nan zamu gane hikimar fifita kasonsa a kan kasonta.

2 - namiji yana anfanin mamaci a rayuwarsa galibi fiye da mace; dan haka babu mamaki idan an fifita shi a kanta a cikin dukiyar da ya bari; Allah Ya yi nuni ga hakan yayin da Ya ce: «Ubanninku da 'yã'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. » (suratul Al-Nisa 11 ); ayar tana nuni ga yin la'akari da wanda ya fi anfani ga mamaci a wajen raba gado.

3 – namiji ya fi sanin hanyar habaka dukiya da tattalinta domin ta anfani al ummah; saboda mace galibi za ta saka dukiyarta ne cikin ababen da ba su da wani babban anfani ga al ummah.

Abu na uku: shi muslunci yayin da ya yanke baiwa mace rabin kason namiji – a cikin halaye sanannu – ya dauke mata nauyin tsiyarwa, da wahalar taje tayi aiki, ko da kwa ta kasance mai dukiya ce; wannan kwa shin ta kasance 'ya ko 'yar uwa sai nauyinta ya kasance akan babanta ko dan uwanta, ko kuma ta kasance mata inda nauyinta zai kasance a kan mijinta ko 'ya'yanta.

Kenan shi muslunci ya dauke wa mace nauyi na ciyar da dukiya a gurare da yawa, yayin da akasin haka ya dora wa namiji nauyi mai yawa; shi yake badawa, mace kwa amsa take. ka ga kwa akwai banbanci tsakanin mai bayarwa da mai amsa; kuma yana cikin adalci a baiwa wanda ke da nauyi a kan sa fiye da wanda ba shi da nauyi.

Dan haka lalle wannan shubuha da makiyan musulunci suke yadawa    - wadda kuma wasu jahilai suka dauka suke yadawa - bata wuce hayaniya ta banza ba.