Sifar hajji


Hajji

Hukunce hukuncen hajji:

Allah Ya farlantawa musulmi ya yi Hajj so ɗaya a cikin rayuwarsa, dan haka za mu yi taƙaitaccen bayani akan aikin hajji, musamman abubuwa masu muhimmanci a ciki, wannan kwa dan sauƙin fahimta.

 

Farkon hajji:
Idan ka yi niyar Hajji sai ka kama hanyar Makka, ka bi ta miƙatin garinka, anan zaka sanya harami kuma ka dauki niyar hajji, ka yi talbiya kana mai cewa:

(labbaikal lahumma labbaik, labbaika la sharika laka labbaik, innal hamda wan ni'imata laka wal mulk, la sharika lak)

Ma'ana: Allah na karɓa kiran Ka bayan karɓawa, Allah na karɓa kiran Ka, ba Ka da abokin tarayya, lalle dukkan yabo da ni'ima na kai daya ne, haka ma mulki na Ka ne, ba Ka da abokin tarayya.

 

Ababen dake haramta bayan daukar harami

Idan ka shiga aikin hajji ya haramta akan ka: farauta, askin gashi a jikin ka, sanya turare, Tarawa da iyalinka, neman aure, sanya rawani, ko riga, ko wando, ko burnishi, ko khuffi.

Mace kwa ba za ta sanya niƙabi, ko safar hannu ba.

Bayan ka gama aikin hajji ya halitta ka aikata duk waɗannan ababe da suka gabata, wadanda sune ababen dake haramta bayan daukar harami.

 

:• Ranar Arafa

A rana ta tara ga watan Zul- Hijjah sai ka tafi Arafa, a can zaka sallaci azahar da la'asar a lokaci guda, raka'a biyu biyu tare da jama'ar musulmi, ka yi ƙoƙari kuma wajen ambaton Allah da roƙon Sa a wannan wuri har rana ta faɗi.

 

• daren Muzdalifah :

Sa'annan ka tafi muzdalifa inda zaka sallaci magriba da isha'i, kuma bayan ka tashi daga bacci ka sallaci asubahi, sai ka ambaci Allah, kana mai yawaita roƙon Sa.

 

• Ranar Hajj mafi girma ko  kuma ranar idi

Bayan sallar asubahi sai ka tafi Mina, ka yi jifa a babban wurin jifa wanda ke shine yafi kusa da Makka, ka jefa duwatsu ƙanana (wanda suka ɗara kashin awaki da kadan), duk lokacin da ka jefa guda sai ka yi kabbara, idan ya kasance kana da abin yanka (tumaki ko awaki ko shanu ko rakumi) sai ka yanka, kana mai neman kusanci da ita zuwa ga Allah, bayan haka sai ka yi aski ko saisaye, sa'annan ka je ka'aba wadda ita ce ɗaki na farko da aka gina aban ƙasa, ka kyewayata (ɗawafi) so bakwai, kana mai farawa daga baƙin dutse dake sukurwar ka'aba, kuma nan ɗawafin ke ƙarewa.

A cikin ko wane kewayo ka ambaci Allah iya ikon ka, kuma ka roƙe Shi abinda ka ke so na alkhairin duniya da lahira, wannan kwa ana kiran sa ɗawafin hajji, sa'annan ka yi raka'a biyu bayan makam Ibrahim, bayan haka sai ka je, ka yi safa da marwa so bakwai (daga wannan dutsen zuwa wancan shine daya, ba zuwa da dawowa ba).

A cikin ko wane tafiya tsakinin duwatsun nan za ka yi ta ambaton Allah iya ikon ka, kuma ka roƙe Shi abinda ka ke so na alkhairin duniya da lahira.

Wannan shi ake kira sa'ayin hajji.

Kuma da haka ne ayukkan da ke kan ka a wannan rana suke ƙarewa; su ne kamar haka: jifa a babban wajen jifa, yanka, ɗawafi, sa'ayi, aski ko saisaye.

Kuma ya halitta ka gabatarda wani aiki akan wani.
 

•ranekun tashriƙ

Sa'annan ka koma Mina, ka yi kwana na goma sha ɗaya, da sha biyu, bayan shigar lokacin Azahar sai ka je ka yi jifa, ka fara da wurin jifa da ke zomaka a farko idan ka taho daga Mina, sai mai bi masa, sa'annan na karshe wanda ka jefa ranar farko, ko wane zaka jefa 'yan duwatsu ƙanana guda bakwai kana mai cewa: Allahu akbar, kuma ka yi adu'a bayan na farko da na biyu.

Idan kana so ka bar Mina bayan kwana na sha ɗaya da sha biyu; dole ne ka fice daga Mina bayan jifar ranar sha biyu ga wata, kafin rana ta faɗi, ka je ka yi ɗawafin bankwana ( kewaya bakwai ) kafin ka koma garin ka.

Bayan ka yi dawafin nan sai ka koma garin ka kana mai fatan Allah Ya karɓa maka, kana kuma mai neman yardarSa, da shafe maka zunubban ka, ka koma tamkar ranar da ma'aifiyarka ta haifeka; musamman idan baka tsutar da kowa ba.

Wannan shine hajji a sauƙaƙe.

 

Ire iren hajji guda uku ( ifradi- ƙirani- tamattu'I )

1- ifradi

Sifar hajji da ta gabata babu umara a cikin ta.

Umara a taƙaice ita ce kamar haka:

Ka ɗau harami, sa'annan ka yi ɗawafi tamkar ɗawafin hajji, kuma ka yi sa'ayi tsakanin safa da marwa kamar sa'ayin hajji, a karshe ka yi aski ko saisaye.

Dan haka sifar hajjin da ta gabata ita ce ake kira (ifradi); saboda ba ka hada hajji da umara ba.

Kuma wannan ifradin shine kaɗai wanda idan ka yi shi yanka ba ya wajaba a kanka.

Amma tamattu'i da ƙirani idan ka yi su wajibi ne ka yi yanka, ka yanka wani daga cikin dabbobin ni'ima.


2- tamattu'i:

Idan kana son ka yi umara tare da hajji; sai ka fara da umara, bayan ka ƙare sai ka zauna a Makka har ranar takwas ga Zul – hijja; a wannan ranar ayukan hajji ke farawa, da haka kenan ka raba umara da hajji.

Wannan kwa shine malamai ke kira (tamattu'i); saboda ka ji daɗi da turare da iyali … tsakanin hajji da umara a cikin tafiya guda.

 

3- ƙirani

Akwai nau'in hajji na uku wanda ke shi ake kira ƙirani, wanda shine haɗa hajji da umara ba tare da jin ɗaɗi tsakanin su ba; sai ka aikata abinda mai aikin hajji ba tare da umara ba yake yi, amma ranar goma sai ka yi niyar ɗawafi na hajji da umara, ka kewaya ka'aba so bakwai, haka shima sa'ayi sai ka yi niyarsa na hajji da umara a lokaci guda.

Da haka faralin hajji ya ƙare, kuma shine ginshiƙi na biyar na muslunci.

kasancewar muslunci shine meƙa wuya; za ka ga alhaji yana meƙa wuyansa gaba ɗaya ga Allah, koda kuwa bai san hikmar wasu daga cikin hukunce hukuncen hajji ba; don kasancewar ya san cewa shi bawa ne na Allah ya wadatar da shi daga sanin hikima; domin idan bawa ya meƙa wuya ga mahaliccinsa sai ubangijinSa Ya yarda da shi, kuma Ya bashi ni'ima mai dawwama a Aljanna.

 

Nafilolin hajji:

Akwai wasu ayukka a hajji, amma ba su zan wajibi ba, duk da cewa akwai lada mai yawa a cikin su, kamar:

Sumbatar baƙin dutse, shan ruwan zamzam, sassaka a inda ake sassaka a cikin ɗawafi da sa'ayi, adduo'i da zikiri na musamman a wasu wurare da wasu lokutta, da abinda ya yi kama da haka.

Akwai kuma hajji na nafila wanda ba farilla ne ba, za'a iya yinsa ifradi ko tamattu'i ko ƙirani, kuma wanda ya aika shi yanada lada mai girman gaske.