shin a kwai Allah koko a'a?


Ni da kai za mu yi tarayya cikin wannan balaguro na bahasin sanin hakika (shin a kwai Allah koko a'a?).

Hakika na san cewa wannan balaguro - na tunani game da abinda ya shafi rayuwarka – yana da muhimmancin da wani balagura ba ya da shi.

Lalle kuma wannan balaguro ne mai da'dada rai na dan adam a cikin wannan duniya mai tafiya a kan tsari mai kayatarwa, mai ban mamaki.

Wannan kwa domin mu yi tunani na hankali, wanda zai aikata kwakwalwa, ya kuma rayar da zuciya; domin mu samu lura game da wadannan ababe da ke kewaye da mu; ma su tafiya a bisa wani tsari mai kyau mai kayatarwa a cikin wannan duniyar mai fadi.

Ababen da za mu yi anfani da su wajen sanin hakikanin wannan lamari da muka ambata, sune ababen da muka mallaka wadanda suke bamu damar riskar al amura, kuma da hankali mai taimaka mana akan tunani da bahasi, da kuma zuciya wadda da ita ne muke shu'uri da riskar hakikanin al amura.

A cikin wannan tafiya ba za mu dora ma wani da ke tare da mu abinda ya fi karfinsa ba, kuma ba za mu dora masa nauyin samar da ababenda da sune za mu kai ga hakika; domin yana daga hakin ko wane mutun – ko kaka matsayinsa yake ta bangren tunani ko wayewa ko zamntakewa …– isa zuwa ga hakikar wannan lamari, ko da kwa bai san kome ba game da yanda aka gina jikin mutun, da ababen da kwayoyin halittar sa suka kunsa, da yanda ake sarrafa makamashi a cikin kwayoyin halittar,  ko kuma bai san kome ba game da ilimin duniyar taura'ru.

Bahasin mu zai kasance akan hakika kamar yanda muke riskar ta ne da bangarorin jikin mu a cikin:

1 – kanun mu, mu 'yan adam.

2 – kauni da ke kewaye da mu.

Wadannan kwa suna bujurowa ga bangarorin jikin mu dare da rana, kuma ba sa bukatar wani dogon ilimi, ko dogon tunani, ko kuma wasu kafofi wadanda su ka ci gaba.

Sai mu fara balaguron mu na neman hakika daga tasha ta farko:

Hakika a cikin rayuwa:

Sai mu tsaya mu yi tunani game da rayuwa da ababen da ta kunsa; za mu ga cewa: rayarwa da kashewa ababe ne ma su konkomuwa a cikin ko wane lokaci, kuma ababe ne da dan adam ya ke gani kuma yake riska da hankalinsa, tare da cewa kuma ababe ne ma su dimautar da riskar hankalin dan adam; abinda zai sa ya maida lamarin zuwa ga wani wanda ya fi karfin dan adam ko wani abin halitta.

Mu ba mu san wani abu ba game da hakikanin rayuwa da hakikanin mutuwa har zuwa wannan zamani, amma muna riskar rayuwar da mutuwa a cikin rayayyu da matattu.

Sa'annan lazimi ne akan mu mu mayar da tushen rayuwa da mutuwa zuwa ga wani karfi wanda ke sama da irin wanda mu ka sani ..

Kai mai rai ne, to wanene Ya saka wannan rayuwar a cikin ka?

wanene Ya samarda wannan abin, wanda ba bu shi a cikin ababen da ke cikin kasa da doron ta, na daga ababe da babu rayuwa a cikin su?

Lalle dabi'ar rayuwa wani abu ne da ya sha banban da dabi'ar mutuwa wanda mu ke gani a tare da ababe wadanda ba su da rai, wadanda ke kewaye da mu .. to ita rayuwar nan daga ina ta zo?

Daga ina wannan rayuwar da ta sha banban da mutuwa ta zo? Lalle ta zo daga Allah ma daukaki ne … wanan ita ce amsa ta kusa .. wanda ya yi musu kwa sai ya bamu amsa!

Mu dibi malamin nan mai bincike akan halitta wanda ake kira "Darwin", wanda ya yi ta tunani game da yin halitta har ya isa magaryar tukewa, sai ya tsaya a can.

Lalle shi ya jahilci halitta tun matakin kwayar halitta ta farko, sai dai ba ya son ya sallama, ya kuma yarda da abinda riska na dan adam ya kamata ya sallama da shi, alhali kwa wannan wani abu ne wanda yake a bayyane; wannan abin shine kasancewar lalle akwai Wani wanda ya busa rayuwa a cikin kwayar halitta ta farko.. ba ya son ya sallama da ababen da ba na nazari da bincike ba ne ba; a'a na tarihi ne game da ja in ja tsakanin su da coci! Sai ga shi yana mai cewa: "lalle fasarar al amuran rayuwa da samuwar mahalicci tamkar shigar da wani abu ne wanda ba ya cikin dabi'a a cikin ababe wadanda muke ganin aikin su a bayyane (ma'ana: Ya zo ya aikata a fili muna ganinSa)!".

To wane aiki a bayyane fili za mu nema a cikin aikin Allah!

Aiki a bayyane kamar yanda yake nihi na ababen halitta ya koru daga mahalicci: Shi ne Ya halicci rayukan su; suna rayuwa, suna mutuwa ba tare da mun ga yanda hakikanin lamarin yake ba.

Shi ma da kanSa yana kauda kai ne, ya ki yarda da abinda fidira ke nuna masa, fidira da Allah Ya halicci dan adam akai; dan haka yana maida asalin halitta ga abinda ke gaba da kwayoyin halitta na farko, abinda ya ke kira: "sababi na farko"! amma ba tare da tambaya ba akan menene sababi nan na farko? Menene sababin nan da ke iya bada rayuwa? Sa'aanan wannan sababi yake da damar – kamar yanda shi Darwin" yake gani – jujjuya kwayoyin halittar nan har ta kai sifa ta karshe! Lalle wannan kaucewa gaskiya ne tare cewa ta bayyana!!!

Hakika sirrin rayuwa shi kadai ya kai mu'ujiza, samarda ita da kuma yanda take zuwa, kuma hankali ba ya daukar kokarin danganta ta ga wani wanda ba mahalicci ne ba.

Kana gani kaka Yake fara halitta! Kana ganin ita wannan rayuwa cikin itaciya mai dada girma, da kuma cikin kwai da jariri, da kuma dukkan abinda ya samu bayan babu shi. Wannan kwa abu ne wanda ikon 'yan adam in sun taru baki daya ba za su iya samarwa, ko su yi da'awar sun samar ba!

Shin an halicci 'yan adam ba daga wani abu ne ba? ko kuma su suke halitta?

Sa'annan ya kai mai neman hakika da gaskiya kayi nazaki a kan karan kan ka ..

Mutun shine abin mamaki ma fi girma a cikin wannan kaunin. Lalle shi abin mamaki ne dangane da yanda aka gina jikinsa, da sirrorin da ke cikin gangar jikinsa, da ruhinsa, lalle mai bada mamaki ne dangane da zahirinsa da kuma badini. Lalle shi mutun yana wakiltar dangogin ababe da ke cikin wannan kauni da sirrorinsa.

Kuma duk inda mutun ya tsaya yana mai tunani gameda ababen al ajabi dake cikin halittarsa zai hadu da sirrori masu ban mamaki da wuce tunani. Yanda aka tsara gabban jikinsa, ayukan gabban jikinsa, da kuma yanda suke gudanar da ayukkan nasu. Yanda tumbi yake nike abinci kuma jijiyoyi na jiki su tsotse tacaccan abincin nan. Yanda mutun yake lunfashi. Yanda jini ke gudana a cikin jikinsa. Yanda jini ke kai kawo tsakanin zuciya da sasannin jiki. Kwakwalwa da yanda take jagoroncin sauren sasannin jiki, kuma take aike masu da sakonni. Jijiyoyi da yanda suke fitar da sinadarai wadanda jiki yake bukata wajen ci gaba da kariya da nashadinsa.

Tafiyar da dukkan wadannan ababe a bisa tsari wanda ya kai ma tuka, wanda ba ya karo da juna, abu ne na al'ajabi. Kuma ko wane bangare na jiki idan ka tsaya ka yi tunani akai za ka ga cewa yana tare da wani abu na al ajabin gaske, amma wannan ga ma su hankali.

Riskar ababe da hanyar riskar, tare rike su a cikin kwakwalwa, kuma maido da su..  a ina ne wai suke a ajie? Kuma kaka suke a ajie? Wadannan hotuna da ababe da aka riska kaka suka like cikin kwakwalwa? Kuma a ina ne a cikinta ? Kuma kaka suke dawowa yayin da aka bukace su?

Sa'annan sirin shi wannan jinsi na dan adam gameda yaduwar sa ta hanyar haihuwa da kuma gadar da dabi'u daga iyaye zuwa ga 'ya'yan su kamar yanda suma suka samo daga iyayansu… ina ne shi wadannan dabi'u suke a ajie a cikin kwayar halittan nan kankanuwa?

ina ne shi wadannan dabi'u suke a ajie a cikin kwayar halittan nan kankanuwa?

Kaka kuma ita kwayar halittan nan ta bibiyo salsalar iyaye da kakannu, ta dauko dabi'un su ba tare da kuskure ba? Kuma ta sake bada mutun mai dauke da irin wanccen dabi'u?!

Kuma mu yi nazari gameda lokacin da jariri yake soma rayuwarsa akan kasa, bayan ya futo daga cikin uwarsa, kuma rayuwarsa ta rabu da rayuwar mamarsa; aka baiwa zuciyarsa da hunhunsa dama ta kebanta da rayuwa. Lalle nazari akan wannan lokaci abu ne mai ban mamakin gaske tare da dimatar da kwakwalwar mai hankali, abinda zai sa mai hankali ya sallama, ya kuma yi imani; domin abin ya fi karfin abin halittaa!

Kuma wata tsayuwar tare da nazari gameda lokacin da harshen jariri yake fara motsi domin ya firta wasu kalimomi da wasu maganganu: ya fitar da sauti daga makogaro, harshe kuma ya fitar da su a Magana.. lalle abun mamaki ne. abun mamaki wanda ba ma lura da shi; domin abu ne wanda yake faruwa ga kowa. Amma idan mu ka yi nazari za mu ga cewa abun mamaki ne da ya kamata hankali yayi tunani a kai; saboda ba kowa ke iya tsara wadannan ababe in ba mahalcci ba.

Kuma ko wane yanki na daga rayuwar abin halita ta na tsayar da mu akan wani abu da ya wuce hankali, abun mamaki matuka.

Kuma jinsin ko wane abu duniya ce ta mamaki; yana bamu hoto na musamman game da wannan duniyar, kuma hoto wanda ba za mu same shi a wurin waninsa ba.. misali zanen yatsu na kowa ya sha banban da na wanin sa, dan haka ka ga na kowa duniya ce kebabbiya wadda ba ta maimaituwa a doron kasa kuma a ko wane lokaci!

Lalle lokaci ne mai kayatarwa, lokacin da dan adam yake tunani game da huskoki na halitta da banbance banbancen su, da al a'dun su, tunani na neman hakika ba tare da son rai ba… to wanene Ya halicci wannan mutun mai bada al ajabi?

Dan haka yanzu ka zo mu je tare da kai zuwa tasha ta biyu a cikin balaguron mu na neman hakika..

Ita ce: ababen da ke cikin kauni (duniya):

Yayin da dan adam yake yawo da idanunsa, da kuma basirarsa - daidai golgodo - a game da ababen da ke da kwai a cikin kaunin wannan mai girman gaske, zai ga alamun kudura mai girma suna bayyana a cikin ababen halitta manya da kanana..

Wannan kaunin da ya kunshi halittu daban daban wadanda ba sa kilguwa, kuma wadanda ake tafiyarwa a bisa tsari abin kyatatawa, wanda ba tangarda a game da shi, kuma ba bu cin karo da juna tsakanin su, ko tsayawa daidai da 'yan mintina.

To lalle dabi'ar wadannan ababen halita yana aiko mana sakon mai cewa: al amarin ba na wasa ba ne ba, kuma ba wai abu bane da ke gudana ba tare da nufi ba.

Wanene Ya samar da dukkan halitta?

Wanene Ya samar da kyawo a game ita halittar?

Kuma wanene Ya shiryar da halittar ga abinda dan shi ne aka halicce ta?

Ya kai mai neman gaskiya Ka yi tunani game da kasa..

Wannan abin halitta (kasa) da aka tanada domin rayuwa, an saka dukkan abinda rayuwar ta ke bukata a cikin ta, a bisa wani tsari wanda mu 'yan adam ba mu ga fiye da shi ba; ga fili mai fadi, tare da taurarun sa wadanda suke tsaye a guri guda da kuma ma su tafiya, wadanda adadinda aka sani kawai ya kai daruruwan milyoyi - tare da cewa wanda ba' a saniba ya fi haka -.

Amma tare da yawan wannan adadi, mu diba mu gani kasa ita aka zaba domin ta karbi wannan rayuwa. Inda kuma wani abu guda daga cikin ababen da kasa ta kebanta da su zai samu cikas da rayuwa ba za ta samu ba a ban ta..

Inda girman ta zai karu ko ya ragu, ko da nisanta daga rana zai karu ko kuma ya ragu, ko da girman rana ko zafinta zai canza, ko motsinta ko kuma tafiyarta zai canza …

Inda girman wata ko nisansa…

Inda yawan ruwa da iska da … za su ragu.. da rayuwa ta gagara.

Shin wadannan ba abubuwa ne da muke gani yau da kullun ba?

Shin wanene Ya halicci kasa?

Wanene  ya bata duk wadannan kebance kebance?

Sa'annan kwayoyin abinci dake cikin kasa soboda halittun da ke cikinta da banta, ko da suke tashi cikin balbalinta, ko kuma suke lunkaya a cikin ruwanta..

Wadannan kwayoyin masu yawan gaske dake tafiya kan wani tsare mai kyawo mai kayatarwa…

Wanene Ya bata (ita kasa) wadannan kwayoyin?

Ka yi tunani - ya kai mai neman gaskiya - game da yawan ababen dake kan kasa, da sassabawarsu, kuma ababen al ajabi dake tare da wadannan ababen wanda ba sa kare wa: duwatsu, da koguna, da tekuna, da gonakai na dabino…

Ko wane daya daga cikin wadannan ababe lalle gonin hannu ne Ya samarda shi. Idan ka yi nazari game da hako sai kaga wata aya, idan kuma ka zo wajen hodama sai ka ga wata ayar daban, sa'annan idan ka dawo ka iske wannan hodama ta bushe sai kaga wata ayar daban alhali kwa baguire guda ne!

Wanene ya kayarta da wadannan ababe?

Kuma ka yi tunani game da halitun dake ban kasa na daga dabbobi da itatuwa, da tsuntsaye, da kifaye, da kwaruka…

Wadannan halittu da ba'a san iya adadin dangoginsu kafin wai daidaikun su ba, kuma kowane dangi daga cikin su al umma ne! kuma ko wane daya daga daidaikun su abun al ajabi ne.

Dukkan dabba, da dukkan tsuntsu, da dukkan itaciya, da dukkan tsutsa, da dukkan gangne, da dukkan fure ..!

Dukkan wadannan ababen al ajabi wanene Ya halicce su?

Ka zo tare da ni, ka yi diba da nazari game da sama...

Ka yi tunani game da tauraru masu kayatar da sama, kayatarwa mai caccanzawa a ko wane lokaci ta bangaren launi, mai caccanzawa tsakanin safiya da marece, tsakanin lokacin bullowar rana da lokacin faduwarta, tsakanin dare mai haske da kuma mai duhu, tsakanin dare a lokacin hazo da lokacin da babu hazo… kai hasali ma kyawansu ya banbanta tsakanin awa zuwa wata awar.. kuma dukkan wannan abubuwa ne da ya kamata su ja hankalin masu lura.

Kuma ka diba wannan falfajiyar sarari mai fadin gaske wadda ido ba ya iya kurewa.. wadda take mai kyawon gani, wadda kalimomi da dan adam yake anfani da su ba za su iya sifantawa ba!

Wannan sararin samaniyar mai cike da ababe ma su kayatarwa, wadanda ke gabanka -ya kai mutun- tambaya ce mai rai da ke neman amsa!

Nan zan tsaya tare da kai ya kai mai neman gaskiya a zangon balaguron mu na karshe…

Bayan wannan yawo da muka yi tare da hankullan mu da zukatan mu, muna masu nazari game da hakika ran dan adam, da hakikar kaunin da muke rayuwa a cikin shi..

Zan bujiro da wata muhimmiyar tambaya… kuma ba shakka amsar tana konkomuwa tare da kai ko da yaushe…

Shin an samar da duniya haka ne ba tare da wani abu ba?

Ko kwa su halittu su suka halicci kanunsu?

Wanene Ya halicci sammai da kassai?

Lalle lamarin samar da rayuwa abin halitta ba ya daawarsa, kuma daawar hakan abu ne wanda hankalin dan adam da fidirarsa ba za su yarada da shi ba, dan haka abu guda zai yi saura shine wanda Al kura'ni mai girma Ya fada: cewa lalle dukkan wannan halittu halittar Allah madaukaki ne, Shi kadai, ba bu wanda yake tarayya da Shi a cikin ta; kuma dan haka Shi kadai ne Ya cancanci a bauta maSa.

Allah da Ya halicce su Shine mahalicci, wadannan ababen halitta kwa sune al'amomin uluhiyarSa da dalilanta a game da kauni da muke gani, saannan kuma game da samuwar dan adam da matakai da yake bi a kansu, wadanda Allah Yake nuna mana a cikin littafiSa  mai girma.

Wadannan ababen halitta masu yawa, wadanda kuma ke dangogi daban daban ta bangaren jinsinsu da girmansu da shakalinsu da ayukkansu… amma wadanda suke tafiya akan tsari guda daya kyakyawa, wadanda suke da tushe guda, kuma wadanda ke amsar umarni daga gareShi, kuma suke mika wuya gareShi suna masu da'a.

Allah.. Shi kadai ne Ya halicci sammai da kassai, da abinda ke tsakaninsu… Shine Ya cancanci wannan sifa madaukakiya.. Allah Shine mahaliccin kome da kowa..

 

Wanda ya hada ya tsara wannan makala shine: Mut'ab Al Harisi.