A cikin wannan kaunin


A cikin wannan kaunin

A cikin wannan kaunin a kwai abubuwa ma su yawa da ake baiwa dan adam ba tare da ya yi wani abu ba, kuma ba tare da ya nema ba; dan haka dan adam a'jizi ne har game da baiwa kansa ababen da ke tabbatar da yawursa.

Misali: rana tana baiwa kasa zafi da rayuwa ba tare da wani kwokari na dan adam wajen neman hakan ba.

Ruwan sama yana sauka, ya kuma baka ruwan da za ka sha, ba tare da wani kwokari daga gare ka ba, kuma ma ba ka da ikon yin hakan.

Iska dake kadawa kewaye da kai; kana shakarta a ko wane wuri ba tare da wani kwokari ko iko daga gare ka ba.

 Kasa tana baka diyan itatuwa bayan kawai ka shuka iri, kuma ka shayar da irin nan; sai ya tsuro ba tare da iko daga gare ka ba.

Kuma dare da rana suna bibiyar juna; domin ka samu damar hutu da tsara rayuwarka; baka zo da hasken ranar ba, kuma baka halicci duhun daren ba. gaka kuma kana mai hutu da dare, ka kuma shagalta da ayukan ka da rana, ba tare da cewa kana da hannu wajen tafiyar da wannan kaunin ba.

Kuma ta hanyar rana da wata kana sanin lokaci da ranekun ka, ba tare da cewa kai kana da hannu game da samar da su ba.

Dukkan wadannan abubuwa dan adam bai halicce su ba; kuma makamantan su suna da yawa.

Duk wadannan abubuwa - dama wasun su da ba su kilguwa - dan adam bai halicce su ba, an halicce su domin shi ne, ba tare da wani kwokari daga gareshi ba.

Shin wannan ba ya sa mu, mu yi godiya ga Allah a bisa wadannan ni'imomi, kuma muyi anfani da su a cikin abinda ke da anfani ga dan adam a cikin wannan kaunin? lalle wannan ya cancanci dole godiya ga Allah madaukaki.

Babu wani - duk inda iliminsa ya kai - da zai iya da'awar cewa shine ya halicci rana, ko kuma ya samar da tauraru, ko kuma ya halicci kasa, ko kuma ya sanya dokokin da halittun wannan kaunin suke tafiya akai… ko kuma ya halicci kansa koma wanin shi.

Dukkan wadannan ayoyi suna tabbatar mana cewa a kwai wani mahalicci ma daukaka, wannan ya samarda su.

A cikin wadannan ayoyi a kwai ma su motsi, kamar yanda ke da koy wadanda ba sa motsi; dukkan su suna tunatar da mu da Mahaliccin mu ne.

Rana tana bullowa da safe, kuma ta fadi da marece… dare da rana suna bibiyar juna… ruwan sama yana sauka… tsirrai suna futowa daga cikin kasa… dukkan wadannan suna tunatar da mu da mahalliccin mu ne, da kudurar Sa, da iradar Sa! Wanene ya tsara fotuwar ranan nan da faduwar ta a bisa tsari mai kayatarwa?! Wanene Ya tsara bibiyar dare da rana? Wanene ya saukar da ruwan nan daga sama, kuma ya tsirar da tsirrai mabambamta?!

Dukkan wadannan suna tunatar da mu da mahallicin mu ne, kuma suna tunatar da mu wajabcin godiya ga mahaliccin mu game da rayuwar da ya arzuta mu da ita, da kuma ayoyin da ya sanya mana a cikin rayuwar.

Allah ma daukaki kafin Ya halicce mu Ya halicci ni'imomi da ke wajabta mana gode maSa: Ya halicci sammai, da kassai, Ya samar mana ruwa da iska, Ya kuma sanya abincin mu har tashin kiyama cikin kasa… dukkan wadannan suna wajabtar mana godiya ga Allah.

Haka ne Allah Ya baiwa dan adam ni'imomi da zaran halittar sa a cikin uwar sa; Ya samar da shi a cikin ma;aifa wadda ke ta yi daidai da rayuwar sa, wadda ta kunshi abincin sa har lokacin da za' a aife shi.

Bayan ya futo daga wannan ma'aifa kuma sai Ya tanadar masa da nono na uwa, wanda ba ya tsaya wa sai lokacin yaye!

kuma ya tanadar masa iyaye ma su kula da shi har lokacin da zai iya kula da kansa.

Duka wannan ni'imomi kafin dan adam ya kai matsayi na dora masa nauyi ne {Godiya ta tabbata ga Allah}.

Hakane zamu ga cewa a kowane lokaci: mi'ima ta gabaci wadannda aka ni'imtar.. mutun lokacin da yake cewa: {Godiya ta tabbata ga Allah}; yana fadar haka ne bayan ababen da ke wajabtar da godiyar suna nan cikin kauni kafin samuwar shi dan adam.

Hasali ma dukkan abinda ka gani a cikin kauni yana wajabtar da godiya ga Allah; amma sai ka ga dan adam yana yabon ita wannan ni'ima yana manta Wanda ya samar da wannan ni'imar!!

Misali: idan kaga wata shuka wace ta kayatar da kai, sai kaga kana cewa: wannan shuka da kyau take, wannan fure da kyau yake… tare da cewa ita wannan shukar, ko wannan fure, ba shi ne ya baiwa kansa wannan kyawo ba, mahaliccinsa shi ya bashi wannan kyawo, kuma Shine Ya cancanci godiyar.

Hanyar manzanni da manhaji da Allah Ya saukar masu ya tabbatar mana cewa lalle Allah ne Ya halitta man wannan kaunin da abinda ke cikinsa kamar yanda Ya haliccemu.. tafiyar wadannan halittu a bisa wani tsari wanda yakai matuka wajen kayatarwa yana nuna mana samuwar mahillici mai girma.. amma shi wannan tsarin ba zai iya futowa ya mana magana ba, dan haka sai Allah YA turo mana manzannin Sa; domin su ce mana: wanda Ya halicci wannan kauni, shine Ya cancanci godiya da dukkan dangogin bauta, ba tare da mun hada Shi da wani a cikin wannan bautar ba.

Sa'annanan manhajin Ubangiji wanda ke cikin Al kura'ni mai girma yana bayyana mana: me Allah Yake so daga gare mu, kuma kaka zamu bauta maSa. Wannan kuma yana bamu damar tafiya a cikin wannan balaguro na rayuwa da zukata wadanda su ke tare da koncin hankali, wadanda su ka kubuta daga dimuwa.. wannan kwa abin godiya ne ga Allah ma daukaki.

Manhajin Allah manhaji ne wanda yake a bayyane, wanda ke hade kowa da kome, kuma wanda ba ya banbanci tsakanin wani da wani; dukkan mu halittu ne gaban Allah, mafificin mu shine wanda ya fi tsoron Allah ma daukaki.

Dan haka shari' ar Allah da dukkan abinda ta kunsa daga Allah ne, amma dukkan wata shari'a koma bayanta aba ce wace zaka samu akwai son rai a ciki; tana la'akari ne da hakkin wadansu yayin da ta take hakkin saura; dan haka ta kunshi zalunci.

Wadanda suke jagorori na gaba gaba a cikin tsarin kasashe ma su tafiya akan tafarkin kominisanci za ka ga sune suke cikin ni'ima da wadata.. yayin da za ka samu sauran jama'a cikin wahala da kuncin rayuwa; saboda sun gina tsarinsu akan son rai da zalunci; dan haka sun gabatar da masalahar su akan kome. Haka ne kuma a cikin kasashe masu tafiya akan tsari na jari hujja, wadanda suke gaba suna fifitar da kanunsu akan gamegarin jama'a.

Amma Allah yayin da Ya saukar da tsarinSa Ya yi hukunci da adalci ne tsakanin mutane; Ya baiwa dukkan mai hakki hakkinsa. Kuma Ya sanarda mu kaka rayuwa za ta mike a ban kasa, ba tare da zalunci ba; wannan kwa abu ne wanda ke wajabta mana godiya ga Allah madaukaki.

Allah Ya cancanci godiya daga gare mu; domin ko da yaushe bamu Ya ke, ba tare da Ya amsa daga gare mu ba, sabanin mu'amala tsakanin 'yan adam; ko da yaushe suna ginata ne a kan masalahar su; domin Allah ba ya bukatar kome daga gare mu, hasali ma Shi ba Ya bukatar abinda ke hannun mu; Shine mai taskokin dukkan wani abu kamar yanda yake cewa: {21. Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne} [al hijr: 21].

Allah ko da yaushe Yana baiwa bayinsa, bayi kwa ko da yaushe amsa suke daga gareShi, dan haka dole ne mu gode maSa.

Allah kuma - tare da cewa Yana bayarwa - Yana son wanda ke tambayarSa sabanin abin halitta.

Allah Yana cewa: {60. Kuma Ubangijinku ya ce: « Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu. »} [ghafir: 60]. Kuma Yana cewa: {186. Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu}. [Al bakara: 186].

Allah kyautarSa ba ta yankewa, kuma taskokinSa ba su karewa; Ya ba bayinSa abinda suke bukata domin su rayu a ban kasa.

Allah Yana cewa: {27. Kuma dã Allah Ya shimfiɗa arziki ga bãyinSa, dã sun yi zãluncin rarraba jama'a a cikin ƙasa, kuma amma Yanã sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, game da bãyinSa, Mai labartawa ne, Mai gani}. [al shura: 27].

Kasance akwai Allah abu ne wanda ke wajabtar mana godiya da yabo ga Allah; haka ma Allah Ya cancanci godiya da yabo saboda zatinSa, da kuma adalcinSa; domin da adalcinSa ne yake kama mai zalunci, Ya masa ukuba a nan duniya domin sauran jama'a su tsorata, wanda kwa Allah bai kama shi akan zaluncin shi a nan duniya Yana jinkirta masa ne har a lahira. Dan haka wanda a ka zalunta yana da yakinin cewa hakkinsa ba zai saraya ba.

Yayin da muke cewa: {godiya ta tabbata ga Allah}, wannan kalimar ta kunshi ababe masu yawa: ta kunshi bautawa Allah, tare da yabonSa, da sonSa, …

Wadannan ababen dukan su suna futowa ne su tabbata a cikin zuciya, sa'annan su bayyana akan gabbai, sa'annan mu ga sakamakon su aban kasa.

Dan haka {godiya ta tabbata ga Allah} ba wai kalimomi bane da ake fada da harshe kawai … a'a kalima ce da ke futowa da ga zuciya,  sa'annan ta bayyana a kan harshe da sauren gabbai, sa'annan mu ga sakamakonta a ban kasa ta hanyoyi daban daban na godiya ga Allah.

Yayin da muka tashi daga barci alhali wasu daga barcin nan sun rasa rayukan su, ya kamata mu yi wa Allah godiya; domin Shi ne ya maida mana rayukan mu. Yayin da muka tashi daga kan kujera Shine Ya bamu dama.. idan muka ci abinci yayin da muke jin yinwa Shine Ya bamu dama … dukkan wadannan ni'imomi suna wajabta mana godiyarSa.

Kai duk wani abu da muka samu damar yi da ganin damarSa ne, kuma ya wajaba mu gode maSa.

{yabo ya tabbata ga Allah} yana nifin yabonSa gameda kasancewarSa Shine kadai Ya cancanci a bauta maSa, domin kalimar {ALLAh} tana nifin abin bauta da gaskiya.

{yabo ya tabbata ga Allah} yana nifin yabonSa gameda kasancewarSa Shine kadai Ya yi halitta, kuma Yake arzutawa, kuma Yake tafiyarda rayuwar su!

Godiya ta tabbata a gareShi saboda Ya halicce mu, kuma Ya bamu matsayi na wadanda Ya baiwa matsayi na daukar nauyin bauta maSa.

{yabo ya tabbata ga Allah} yana nifin yabonSa gameda sunayanSa kyawawa da sifofinSa ma daukaka.

Ni'ima ta farko: ni'imar bamu matsayin bautarSa, wannan kwa babban matsayi ne inda mun kaddara ta yanda ya kamata.

Ni'ima ta biyu: kasancewarSa ubangijin halitta.

A cikin rayuwa a kwai masu da'a, kamar yanda ke da wadanda suka yi tawaye, a kwai muninai, kamar yanda ke da kafirai… wadanda ke shiga cikin baiwar bauta sune muminai. Amma baiwar kasancewarSa Mahalitti mai arzutawa, wannan ya game kowa da kowa ne; dan haka muna godewa Allah a bisa baiwar uluhiyarSa, da baiwar rububiyarSa, da kuma ni'imar sanarda mu sunayenSa da sifofinSa!!

Kome yana tafiya ne a bisa tsarinSa da ganin damarSa, babu wanda ya isa ya kiya. Rana ba ta iya kin bullowa ko faduwa, kasa ba ta iya hana futowar tsirrai, kauni ba ya iya rike iskan dake cikinsa!!

Dan haka Allah Yana kwantar da hankulan bayinSa su san cewa Shine ubangijin wannan kaunin; dan haka ba bu wani daga cikin ababen da Allah Ya saka a cikin wannan kaunin, da zai iya hana Anfana da su.

Dan haka sai mu gode maSa musamman ma idan muka diba yanda Ya saka mu shugabanni akan sauran abin halitta.

Shi kuma sakamakon bautar nan za mu same shi a gidan lahira; domin gidan duniya gidan zabi ne tsakanin imani da rishinsa, dan haka wasu suke kin yin imani, kuma duk da haka Allah Ya daidaita su da muminai ta bangaren arzutawa da abinda ya yi kama da haka. Amma a lahira kyatar Allah tana takaita a kan muminai ne, kafirai ba su da rabo a ciki.

Idan ya kasance dukkan ni'imomin Allah suna bukatar godiya, haka ne {mamallakin ranar sakamako} Ya cancanci godiya mai yawa … saboda inda bai sanya ranar sakamako ba; da wanda ya aikata sharri a rayuwarsa ya tsira da zaluncin sa, ba tare da an sakauta masa ba. kuma da wanda ya yi da'a ga Allah ya bi umarninSa ya wahaltar da kan sa ba tare da wani sakamako ba..

Amma dake Allah Shine {mamallakin ranar sakamako} sai ya sanya adalci a cikin halittarSa. Da wannan adalcin sai Ya kare hakkin mai rauni da dukkan wanda aka zalunta; domin akwai ranar sakamako da zai sakautawa kowa a bisa aikinsa.

Sa'annan wanda ya tsaya akan hanyar Allah da tsoron Shi, tsoron nan na shi yana anfanin waninsa; domin zai baiwa kowa hakkin sa, kuma ya yi afuwa da yafewa.. dan haka dukkan wanda ke kewaye da shi zai anfana da shi.

Shi kwa wanda ke mai sabo, sabonsa yana shafar kowa da kowa ne;  haka {mamallakin ranar sakamako} shi ne ke nuni ga mizani. Ka yi imani da cewa mai zalunci sakamako yana jiransa, ba ya iya kaucewa duk yanda karfinsa ya kasance, dan haka sai ka samu nutsuwa da koncin hankali.

Za mu iya ci gaba da zana ni'imomin Allah ba tare da mun kai karshe ba, domin ni'imominSa ba su da iyaka.. kuma ko wace ni'imar tana sanarda mu ne cewa akwai Allah, kuma tana ba mu dalili na imani da cewa shi wannan kaunin yana da mahallici wanda ke mabuwayi, kuma babu wanda zai iya da'awar cewa shine Ya halicci wannan kaunin ko abinda ke cikinsa.. wannan abu ne wanda ke an rigai an yanke shi.

Godiya kuma ta tabbata ga AllahWanda Ya saka imani a cikin zukatan mu, kuma Ya karfafa wannan imanin da ayoyin da ke cikin kauninSa, wadanda ke nuna mana samuwarSa da ikonSa, dan mu kadaitar da Shi da bauta.

 

Marji'in tsara wannan makalar shine: tafsirin shaihun malami Muhammadu Sha'arawi ( Allah Ya masa rahama), suratul fatiha.