Dalilai na hankali a cikin Al ƙur'ani Mai Girma da ke tabbatar da ranar hisabi ta hanyar wasu sifofin Mahallaci


     Maƙa'la taƙaitatta gameda dalilen Al ƙur'ani Mai Girma na hankali ma su tabbatar da ranar hisabi ta hanyar wasu sifofin Mahallaci.

Dukan yabo ya tabbata ga Allah Wanda Ya sifanta da sifofin kamala, kuma tsarki ya tabbata ga wanda Ya tsarkaka daga dukan nakasa.

Muna shaida cewa ba wani abin bauta na gaskiya banda Allah, Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya; Shi Ya yi halitta, kuma Ya  ke halitta, Shi ke umarni, Shi ke hisabi.

Kuma muna shaida cewa Muhammad annabi ne, kuma manzo ne na Allah, tsira da salama ta Allah su tabbata a gare Shi.

Allah muna roƙonKa Aljanna, kuma muna neman tsarinKa daga wuta.

Wannan maƙa'la ce taƙaitatta game da a'yoyi na Al ƙur'ani Mai girma waɗanda a cikin su akwai dalilai na hankali da ke tabbatar da ranar hisabi (sakamako); ta hanyar tabbatar da samuwar Mahalicci, ko ta hanyar tabbartarda wasu sifofin Sa; ga misali: hikma, da ilimi, da mulki, da jiɓintar al amurra, kasancewar Sa Shi kaɗai ne Mahalicci, Mai mulki, kuma Mai tafiyar da al amurra, da ƙaddara su.

Dan haka wannan maudu'i zai huskanci dangogi biyu ne na mutane:

1-waɗanda suka yi imani; dan su ƙara imani.

2-waɗanda suka yarda da cewa akwai Mahalicci, amma ba su yi imani da ranar sakamako ba.

Mahalicci Shi Ya yi halitta gaba ɗaya, ko wane dangi na halitta Ya yi miliyoyi irin Sa, akwai al ummomi na 'yan adam, da dabbobi, da tsirrai, da ababen da ba su motsi.

Acikin wannan akwai dalilai na hankali ga dukkan mutane, a ko wane lokaci da ko wane guri, akan cewa ba bu abinda zai hana ci gaban Mahalicci da yin halitta; kuma da tada matattu domin Ya masu hisabi; Shine mahallici wanda Ya yi halitta, kuma Yake ci gaba da yin halitta.

Allah Maɗaukaki Yana cewa: {shin , kuma Wanda  Ya halitta sammai da ƙasa bai zama Mai ikon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shi Mai yawan halitta ne, mai .[y.s: 81]ilimi}  

{Halittarku ba ta zama ba, kuma tayar da ku bai zama ba, face  kamar rai guda. Lalle, Allah Mai ji ne, Mai gani} ( suratu Lukman: 28 ).

 

 

 

Mahalicci Shi Ya yi halitta gaba ɗaya; Ya halicci ababen halitta dangogi makamanta.

Ko wane abu Ya halacci dangogi sa; Ya halicci maza da mata acikin 'yan adam, da dabbobi, da itatuwa da abinda yayi kama da haka; kuma dukan su suna kafa hujja ne akan ƙudurar Uban giji da ikonSa akan sake maido da halitta bayan mutuwa domin musu hisabi.

{37. Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)38. Sa'an nan ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓoɓinsa; 39. Sa'an nan Ya sanya, daga gare shi, nau'i biyu: namiji da mace? 40. Ashe Wannan bai zama mai iko ba bisa ga rayar da matattu } (suratul ƙiyama).

Mahalicci Shi Ya yi halitta gaba ɗaya; Shi Ya fara halitta.

Lalle duk wanda ya tabbatar da Mahalicci to lalle kuma ya tabbatar da cewa Shine Ya fara halitta; wanda kwa Ya fara halitta yana da iko akan sake maido halittan nan bayan mutawa kamar yanda Ya ga dama.

{kuma Shine Wanda Ya fara halitta, sa'an nan Ya sake ta, kuma (sakewarta) ta fi sauki a gare Shi} (suratur Rum: 27).

Mahalicci Shi Ya yi halitta gaba ɗaya; Shi ne Ya halicci halitta mafi girma.

Wanda Ya ɗau abu mai nauyi maras nauyi ba zai gagare Shi ba, dan haka wanda Ya halicci sammai da ƙasa mai iko ne akan Ya halicci dan adam; kamar yanda Allah maɗaukaki Ya ke ce: {57. Lalle hallitar sammai da ƙasa, ita ce mafi girma daga halittar mutane, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba. 58. Kuma makaho da mai gani ba su daidaita, kuma waɗanda suka yi imani suka aikata ayyukan ƙwarai, da mai munanawa ba su daidaita. kaɗan ƙwarai, kuke yin tunani. 59. Lalle Sa'a haƙiƙa mai zuwa ce, babu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutane ba su yin imani } (suratu Ghafir).  

Mahalicci Shi Ya yi halitta gaba ɗaya; Mahalicci Shi ne Ya halicci yanayin halittu da halayen su. 

Ababen halitta, yanayi da halin su, yana caccanzawa; daga bacci zuwa farkawa, daga ƙarfi zuwa rauni, daga rayuwa zuwa mutuwa, idan ka diba halin wata sai ka ga yana caccanzawa daga haifuwar shi zuwa mutuwa, haka ma rana daga ɓullowarta zuwa faɗuwarta; dan haka a hankalce Mahaliccin da ke jujjuya abin halita daga yanayi zuwa wani yanayin Yana da ikon canza halitta daga hali na rayuwar duniya zuwa ga hali na hisabi da sakamako akan ayukka.

kamar yanda Allah maɗaukaki Ya ce: {3. kuma idan ƙasa aka mike ta. 4. Kuma ta jefar da abin da yake a cikinta, ta wofinta  daga kome. 5. Kuma ta saurari Ubangijinta, aka wajabta mata yin sauraren. 6. Ya kai mutun! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, to, kai mai haɗuwa da shi ne. 7. To, amma wanda aka baiwa littafinsa da damansa. 8. To za'a yi masa hisabi, hisabi mai sauƙi. 9. Kuma ya juya zuwa ga iyalinsa ( a cikin Aljanna, yana mai raha. 10. Kuma, amma wanda aka bai wa littafinsa daga wajen bayansa. 11. To za shi dinga kiran halaka. 12.kuma  ya shiga sa'ir. 13. Lalle ne shi, ya kasance (a duniya) cikin iyalinsa yana mai raha. 14. Lalle ne ya yi zaton ba zai komo ba. 15. Na'am! Lalle ne Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi. 16. To, ba sai Na rantse  da shafaƙi ba. 17. Da dare, da abin da ya ƙunsa 18. Da wata (haskensa) ya cika 19. Lalle ne kuna hawan wani hali daga wani hali } (Suratul Inshikak). 

Mahalicci Shi Ya yi halitta gaba ɗaya; Shi ne Ya halicci mutuwa da rayuwa.

Hankali yana gani kullun mutane da dabbobi suna mutuwa kamar  yanda suke rayuwa, wannan kwa duk yana nuni ne ga cewa Mahallicci Ya mallaki sifar rayarwa da kashewa a ko wane lokaci; dan haka a hankalce ba abinda zai hana Ya rayarda matattu a ko wane lokaci; kamar yanda Allah maɗaukaki ke cewa: {Ranar da kasa ke tsatshagewa daga gare su, suna masu gaggawa. Wancan tarawar mutane ne, mai sauƙi a gare Mu} (Suratu Kaf: 44).

Mahalicci Shi Ya yi halitta gaba ɗaya; Shi ne Ya halicci mutuwa da rayuwa.

Yana daga kamalar Ubangiji caccanza halin rayuwa da mutuwa; Yana rayar da kasa da tsurrai, Wanda Ya rayar da milyoyin tsirrai daga kasa wadda ke matatta Yanada ikon rayarda mutane bayan mutuwar su; kamar yanda Allah maɗaukaki ke cewa: {kuma kana ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsiri daga kowane naui mai ban sha'awa. 5. Wancan ne, domin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne Shi Yake rayar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kome. 7. Kuma lalle ne Sa'ar tashin ƙiyama mai zuwa ce, babu shakka a cikinta, kuma lalle ne Allah Yana tayar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura } (Suratul Hajj).

Mahalicci mai hikima ne

Lalle Mahaliccin da Ya halicci hankullan masu hikma, Ya kuma halicci dangogin hikimar, Ya siffantu da hikima; mai hikima kwa ba  makawa zai sakautawa mai aiki na gari da sakamako mai kyau, Ya kuma sakautawa wanda bai yi aiki na gari ba da sakamakon aikin sa; tamkar shugaba da mabiyan sa na gari da wadanda ba na gari ba.

Mahalicci mai hikima, mai kuma rahama wa muminai, mai kuma ƙarfi akan mujirimai, wanda Ya yi da'awar cewa Mahaliccin nan zai daidaita tsakanin masu aikata alkhairi da masu aikata munanan ayukka; Ya rayarda su haka dan wasa, kuma Ya barsu haka ba tare da hisabi ba, lalle wannan ya tuhumci Mahalicci da sifofin wasa da wauta.

{Shin, to, kun yi zaton cewa Mun halitta ku ne da wasa, kuma lalle ku, zuwa gare mu, ba za ku komo ba?} (Suratul mu'minun: 115).

{27. kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke tsakanin su ba a kan karya. Wannan shi ne zaton waɗanda suka kafirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kafirta daga wuta. 28. Ko za Mu sanya waɗanda suka yi imani, kuma suka aikat ayyukan kwarai kamar wadanda suke masu ɓarna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za mu sanya ma su bin Allah da taƙwa kamar fajirai makarkata } (suratu Sad).

{Shin, kyautatawa na da wani sakamako? (A' aha) Face kyautatawa} (suratur Rahman: 60).

{4.ko waɗanda ke aikata miyagun ayyuka sun yi zaton su tsere Mana? Abin da suke hukuntawa ya munana} (Suratul Ankabut).

Mahalicci mai ilimi ne game da kome

Shugaban ma'aikata idan ya ƙididdige zuwa da rishin zuwa na ma'aikata, nagarta da rishin sa game da ma'aikatan sa, sa'annan bai musu hisabi ba; to lalle ya zama shugaba mai wauta da rishin lissafi; domin ya tattara bayanai ma su yawa ba da wata fa'ida ba.

Haka ne yarda da cewa akwai mahalicci yana wajabtar mana yarda da cewa mai sani ne game da bayin sa da ayukkan su na zahiri da baɗini, duk wanda kwa ya kasance yana da sanin wadannan bayanai game da bayi, lalle ba zai tattarasu ba dan wasa, ba tare da wata hikima ba; abinda zai sa ya tattara su shine dan yayi sakamako da hisabi.

{6. Ranar da Allah zai tayar da su gaba ɗaya, sa'an nan Ya ba su labari game da abin da suka aikata, Allah Ya lissafashi, alhali kuwa su, sun manta da shi, kuma a kan kome Allah Halartacce ne 7. Ashe b aka ga cewa lalle Allah Yana sane da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata ganawa ta mutun uku ba za ta kasance ba face Allah Shi ne na huɗu ɗinta, kuma babu ta mutun biyar face Shi ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kasa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa face Shi Yana tare da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya ba su labara game da abin da suka aikata a Ranar ƙiyama. Lalle Allah Masani ne ga dukan kome} (suratul mujadala).

{3. kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Sa'a ba za ta zo mana ba" ka ce: "kaya! Na rantse da Ubangijina, lalle za ta zo muku". Masanin gaibi, gwargwadon zarra ba ta nisanta daga gare Shi a cikin sammai, kuma ba ta nisanta a cikin ƙasa, kuma ba bu mafi ƙaranci daga wancan kuma babu mafi girma face yana a cikin littafi bayyananne} (suratu Saba')

Mahalicci Shi ya mallaki ƙarshen al amurra, kuma wajen Sa ne makoma take; domin Shine mamallaki, ubangiji, majiɓincin al amari.

Lalle wanda Ya yi halitta Shine Ya mallaketa, kuma a hankalce wata rana zata zo da za su waiwayi Mahaliccin su dan Ya sakauta musu.

Allah maɗaukaki Yana cewa: {81. A'a, sun faɗi misalin abin da na farko suka faɗa 82. Suka ce: "shin, idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasusuwa, shin, lalle ne mu, haƙiƙa wadanda ake tayarwa ne?" 83. "lalle ne, haƙiƙa, an yi mana wa'adi, mu da ubannin mu ga wannan a gabani. Wannan abu bai zama kome ba, face tatsuniyoyin na farko" 84. Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikin ta, idan kun kasance kuna sani?" } (Suratul mu'minun).

Ba makawa wata rana wannan halittun za su koma ga Mahaliccin su domin Shine majiɓincin al amurran su; Shi Yake rayar da su, Shi kuma Yake kashe su, kuma Shine Ya halicce su; a taƙaice dai Shine majiɓincin al amurran su; Shi Ya fitar da shashen su daga shashe, kuma shine ya halicci sammai da ƙasa kuma ragamar su na hannun Sa, arziƙi na hannun Sa, Yana bada shi yanda Ya so, kuma Shine Yake da ƙudura wadda bata da iyaka, kuma Shine Yake da ilimi da ba shi da haddi; ba wani abu da yayi kama da Shi.

Ganin cewa Shine majiɓincin al amurra; ba makawa akwai ranar da za su koma gare Shi domin Shine mamallakin karshen al amurra.

Allah maɗaukaki Yana cewa: {har idan mutuwa ta jewa ɗayan su, sai manzannin Mu su karɓi ransa, alhali su, ba su yin sakaci 62. Sa' an nan kuma a mayar da su zuwa ga Allah Ubangijinsu na gaskiya. To! A gare Shi hukunci yake, kuma Shi ne ma fi gaugawar masu bincike} (suratul An'am).

Kuma ba makawa za su koma ga ubangijin su; saboda su bayin Sa ne, Shi Ya halicce su, kuma Ya tattale su , Shine kuma shugaban su na haƙiƙa, ubangijin talikai.

{10. kuma suka ce: "shin, idan mun ɓace a cikin ƙasa, shin lalle mu, tabbas ne, muna zama a cikin wata halitta sabuwa?" A'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kafirai ne 11. Ka ce: Mala'ikin mutuwa wanda aka wakkala a gare ku, shi ne ke karɓar rayuwar ku. Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku } (Suratus Sajda).

{42. kuma lalle makomar zuwa Ubangijinka kawai } (Suratun Najm).

{ zuwa Ubangijinka wurin tabbata, a ranar nan yake} (Suratul kiyama).

{lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take} (Suratul Alaƙ).

{to, lalle su, suna a cikin shakka daga gamuwa da ubanginsu} (Suratu fussilat: 54).

{ 93. Dukan wanda yake a cikin sammai da kasa bai zama ba face mai je wa mai rahama ne yana bawa} (Suratu Maryam).

Ba wata tatsunniya ko ruhwa ido a game da komawar bayi zuwa ga mamallakin su, kamar yanda waɗanda ke inkarin ranar hisabi suke faɗa.  

Mahalicci Ya ƙaddara kome da kome, dan haka yana daga cikin abinda Ya ƙaddara kasancewar duniya gidan jarrabawa ne.

Wannan jarrabawar kwa tana farawa daga balagar dan adam; kamar yanda Allah Yana cewa: {165." Kuma Shi ne Wanda Ya sanya ku masu maye wa juna ga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sashenku bisa ga sashe da darajoji; domin Ya jarraba ku, a cikin abin da Ya baku". Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggawar ukuba ne, kuma lalle ne Shi, haƙiƙa, Mai gafara ne, Mai jin ƙai} (Suratul An'am).

Kuma Ya ƙaddara jarrabawar nan ta 'yan adam a lokaci sananne.

Allah Yake cewa: {8. Shin, ba su yi tunani ba a cikin zukatan su cewa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abinda ke tsakanin su, face da gaskiya da ajali ambatacce ? kuma lalle masu yawa daga mutane kafirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu? } (Suratur Rum).

Kuma Allah Ya ƙaddara jarrabawar nan ta kare da mutuwar dan adam, babu dawowa bayan mutuwa: {31. ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutanen) ƙarnoni a gabanin su, kuma cewa su ba za su komo ba} (Suratu Y. S)

Kuma Ya yi ababen da jarrabawar nan ke ɓuƙata; kamar samar da ruwa daga sama ko rijiyoyi, samar da abinci daga dabbobi da itatuwa, da inuwar su da hurannin su, da samar da wata da rana da tauraru dan sanin lokutta da sa'sanni, da lokacin shuka, Ya kuma samar da koguna da tekuna da abincin dake cikin su, da ababen ado, ga jiraguen ruwa suna tafiya akai, kuma ya samar da dangin namiji da mace dan su ci gaba da ayayyafa, Ya kuma samar da iska dan su shaƙa su yi lunfashi… kamar yanda Allah Yake cewa: {70. Kuma lalle ne mun girmama 'yan adam, kuma Muka ɗauke su a cikin ƙasa da teku, kuma Muka arzuta su daga abubuwa ma su ɗaɗi, kuma Muka fifita su akan ma su yawa daga waɗanda Muka halitta, fifitawa 71. A ranar da Muke kiran kowane mutane da limaminsu, to, wanda aka bai wa littafinsa a damansa, to, waɗannan suna karatun littafinsu, kuma ba'a zaluntar su da zaren bakin gurtsin dabino 72. Kuma wanda ya kasance makaho a cikin wannan, soboda haka shi a lahira makaho ne, kuma mafi ɓata ga hanya} (Suratul Isra).

{10. kuma lalle ne, hakika, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abubuwan rayuwa, a cikinta; kadan kwarai ku ke godewa} (Suratul A'araf).

Kuma Mahallicci Ya kaddara yawaita hanyoyi da ababen jarrabawa; Ya samar mu ku ababen da za'a iya anfani da su ta hanya mai kyau kamar yanda za'a iya anfani da su ta hanya maras kyau; misali: samun arziƙi ta hanyar halal ko haram, makami za'a iya anfani da shi ta hanyar alheri kamar yanda za'a iya anfani da shi ta hanyar sharri; tamkar kisa da abinda ya yi kama da haka, kamar kuma abinci akwai kyakyawa halal kamar yanda akwai mummuna haram, kuma kamar samar da hanyoyi na aure na halal da samar da hanyoyi na fasiƙanci na haram.

Allah Maɗaukaki Yana cewa: {ko wane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. kuma muna jarraba ku da sharri da alheri domin fitina. Kuma zuwa gare Mu ake mayar da ku} (suratul Anbiya': 35).

A karshe

Wanda ya yi inkarin ranar hisabi bayan waɗannan hujjoji lalle yana rayuwa ne cikin wahami da dimuwa, nesa da haƙiƙanin rayuwa, da hankali, da halitta, kuma ya yi inkari da manta abinda ya tabbatar da shi na cewa akwai Mahalicci, wanda Shine Ya fara halitta, Ya halicci abinda ke ya fi girma, kuma Ya halicci kwatankwacin kome, Ya halicci namiji da mace a kome, Ya halicci dare da rana, bacci da farkawa, mutuwa da rayuwa, Ya tsirar da tsirrai, Ya halacci yanayi da halayen ababen halitta, Ya sifanta da sifofi na hikima da adalci; Yana kyautatawa masu kyautatawa, Yana mai sakautawa masu mummunan aiki da sakamakon aikin su, Shi kuma mai ƙarfin da ba ya da iyaka ne, Shi mai tsananin azaba da uƙuba ne, Ya ƙaddara kome, Shi Maɗaukaki ne babu wani abu sama da Shi, iliminSa da ƙarfinSa da ikonSa, da ganinSa, da jinSa, sun yi kewayo da kome da kowa, ba abinda zai gagare Shi.

Ya san abinda ke ɓoye kamar yanda Ya san abinda ke a bayyane, kuma a hannunSa ƙarshen al amurra gaba ɗaya suke; Shine ma jiɓincin al amurran su; babu wani abu da yayi kama da Shi, Yana jin mu, Yana ganin mu, Shi ya halicci sammai da ƙasa, kuma Shi ke da ragamar su, Shi ke arzutawa; idan Ya ga dama Ya yalwata, ko kuma Ya ƙuntata arzikin wanda Ya ga dama, Shi Ya ke sarrafa haihuwar su kamar yanda Ya ga dama, Shine sarkin da muke tawakkali a gareShi, kuma wajen Shi ne makomar mu take, Shi ne mamallakin kome da kowa, ubangijin talikkai.

Mai inkarin ranar sakamako ya dangana sifar naƙasa ga mahalicci: sifar kasa rayar da mamatu, sifar wauta, da jahilci; dan zai bar halitta hakanan ba da hisabi ba, haka ne ya sifanta Shi da rauni dan ba Ya iya sakautawa mujirimai akan fajircin su, ya kuma sifanta Shi da sifar rishin rahama; dan ba zai sakautawa ma su kyautatawa ba, ya kuma sifanta Shi da sifar talauci; dan ya ce: ba Shine mamallaki ba, kuma ababen halitta ba za su koma gare Shi ba, ya kuma sifanta Shi da sifar bauta; dan ya ce: ba mamallaki ne da za'a koma gare Shi ba, ya kuma sifanta Shi da sifar bin waninSa; dan ya ce: ba majiɓincin al amari ne ba da kome zai koma gare Shi.

Wannan taƙaitattar maƙa'la ce gameda a'yoyi ma su tabbatar da ranar hisabi ta hanyar hankali.