shin a babu tawye Allah daga  kamala a cikin cewa Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) dan Allah ne ?


 

Da sunan Allah mai rahama, mai jin kai

Da sunan Allah majibincin kowa

 

shin a babu tawye Allah daga  kamala a cikin cewa Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) dan Allah ne ?

Lalle crista suna cewa Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) dan Allah ne ! yayin da addinin muslunci yake cewa: Allah ba Shi da da.

Idan muna son mu san inda gaskiya ta ke sai mu yi tunani game da amsar wannan tambayar: kasancewar Allah yana da da, shi wannan yabo ne a gare Shi ko tawaya ne?

Mu yi tunani tare da adalci a kan wannan amsar: kamanta mahalitti da abin halitta wajen danganta maSa da sifa ce wadda ke tare da wasu ababe kamar haka:

1 – samuwar da ya na nuna cewa ma'aifin nan mabukaci ne zuwa ga wannan da; Wannan kwa ya kunshi kasancewar ma'aifin nan bai wadaci kanSa ba. Dan haka ne Alkura' ni ya kawo hujja ta hankali yana mai cewa: {sun ce: Allah ya riki da ! tsarki ya tabbata a gare Shi, Shi ne mawadaci}.

Duk wanda ya ce Allah Yana da, to lalle ya ce Allah ba mawadaci ba ne ba, kuma Allah zai bukaci wani abu, idan kwa ya kasance haka, to lalle a kwai nakasa tare da Shi.

Kaka kuma abin bauta zai kasance a kwai kaskanci tare da shi ? shin zai taba yuwa ?

2 – lalle samuwar da ya na tabbatar da cewa shi mai dan nan mulkin shi ragagge ne … dan shi zai dauki wani abu daga mulkin nan, a karshe kuma zai rasa ko da wani abu daga mulkin nan nashi.

Dan haka ne Alkura' ni mai girma ya zo da hujja ta hankali yana mai cewa: {lalle wadanda su ka ce: almasihu dan Maryam dan Allah ne sun kafirta … mulkin sammai da kasa da abin da ke tsakaninsu na Allah ne Shi kadai}. Duk wanda ya ce: Allah ya na da, to lalle ya ce mulkin Allah ragagge ne, bai mallaki sammai da kasa da abin da tsakanin su ba !!

3 – lalle samuwar da ya kunshi cewa shi mai dan nan ba ya iya tashi da dukkan ayukkan shi; dan haka tilas ne ya bukaci dan nan dan ya taimaka masa.

Wannan a cikin shi akwai sifanta Allah da cewa ba Shi da kudra da iko da jibintar al – amurran duka !

4 – samuwar da ya kunshi cewa mai dan nan zai tsufa kuma zai gaza, dan haka yana bukatar wanda zai taimaka masa a lokacin tsufan nan … domin imba haka ba me zai sa ya riki da ?

Wannan kwa ya kunshi cewa mai dan nan zai rasa sifar ( karfi ).

Wanda kwa ya sifanta Allah da cewa yana da da, hakika ya sifanta Shi ne da rishin karfi, kuma cewa rauni zai riske Shi, kenan kwa a kwai kaskanci tare da Shi.

Shin zai iya yuwa a ce mahaliccin kauni ya kasance ya na tare da rauni ?

5- samuwar da ya na nuna cewa mai dan nan zai mutu … kuma dan shi zai kaje shi.

Wannan kwa ya kunshi cewa uban dan nan zai rasa sifar ( rayuwa ).

Dan haka duk wanda ya ce Allah yana da da, to lalle ya ce Allah ba rayayye ba ne ba, kuma mutuwa za ta riske Shi, dan haka akwai nakasa tare da Shi.

To shin ubangijin sammai da kassai zai kasance nakasashe ?

6 – inda zamu ce: Allah yana da da, sa' an nan wani ya zo ya ce da mu: Allah ya na da mata da mahaifi da jikoki … shin za mu iya musu, ko kwa sai dai mu kale shi mu yi shiru ?

Dan haka ne wannan hujjan ta hankali ta zo a cikin Alkura' ni: « Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa ( Shi ) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da 'yã'ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa.

101. Mafarin halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta dukkan, kõme, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne? ».

Bayan wadannan ababe da muka gabatar za mu samu sakamako na karshe kamar haka: idan mu ka ce Allah yana da da, to lalle mun kamanta Shi da ababen halitta, wadanda ke da rauni, kuma mun raba Shi da dukkan sifa ta kamala.

Amma wanda ya ce Allah ba Shi da da, lalle ya san haka ne ta huskar sanin Allah Shi ne mahalitti, mahalitti kwa ba zai kasance kamar abin halitta ba ko da dai, domin abin halitta ya na da rauni, Allah kwa dole ne Ya kasance:

Mabuwayi,

Mawadaci,

Mai mulki cikekke,

Mai karfi'

Mai kudura,

Mai tsarki,

Mai hikma,

Rayayye kuma mai tsayuwa a kan kome da kowa, …

Da sifofi kamar haka na kamala.

Ya kai dan uwa makaranci, mai neman gaskiya, wannan mas'ala ce wadda ta shafe ka, kadda ka bar hankalin ka wani ya yi wasa da shi, ka tsaya ka yi lissafi a kan shi domin ka isa ga gaskiya tare da hujjoji ma su gamsarwa.

Lalle musulmi su na girmama Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ), kuma suna mutukar son Shi; domin kwa Yana daya daga cikin annabawa, wadanda mutun ba zai taba imani ba muddin bai yi imani da su gaba daya ba.

Dan haka muslunci bai yarda ba wani ya zagi Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ), ko ya kaskantar da Shi, ko ya fadi wata magana ta baci game da Shi, hasali ma wanda bai yi imani da manzoncin Shi ba, lalle ya karyata Alkura' ni da manzon Allah ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ), kuma ya futa daga da'irar muslumci.

Tare da haka kuma musulmi ba sa daga Shi fiye da matsayin Shi na mutun, Shi lalle bawan Allah ne, kuma manzo ne da Allah ya aiko, Allah ya kuma sanya halittar sa aya ce ga dukkan bayin Shi.

Ka tsaya tare da hankalin ka, ka tambayi kan ka game da wadannan ababe:

1 – asarar mi za mu yi idan mu ka ce Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) manzon Allah ne ? shin ba mu girmama Shi ba ?

2 -  dan mi muke karyatar da kanun mu bayan hujjoji sun bayyan cewa Shi mutun ne wanda Allah Ya aiko ? shin fadar cewa Shi Allah ne ko kuma dan Allah ne ba zai fusatar da Ubangijin mu ba ? domin mun sifanta Shi da nakasa !

3 – shi ubangijin bai kebanta ba da kasancewa mahaliccin kauni ba ? dan mi ya sa ba za mu cika tauhidin mu ba da kadaitar da Shi da ibada ba ?

4 – ni'imomin Allah suna sabka gare ka safiya da yamma, shi za ka fuskanci wadannan ni'imomi da tauye Shi daga sifofi na kamala ne maimakon godiya a kan su?

5 – shi ka na tsammanin cewa mujrimai da suka ce Allah ya na da da za su iya boye gaskiya bayyananna tamkar hasken rana ?

A karshe:

Mu yi tunani a kan abin da Allah ya fada a cikin sako na karshe da ya sabkar:

« 88.  Kuma suka ce: Mai rahama Yã riƙi ã! 
89. Lalle ne haƙĩƙa kun zo da wani abu mai girman mũni. 
90. Sammai sunã kusa su tsattsage sabõda shi, kuma ƙasa ke kẽce kuma duwãtsu su faɗi sunã karyayyu.

91. Dõmin sun yi da'awar ɗã ga Mai rahama. 
92. Alhãli bã ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗã. 
93. Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba fãce mai jẽ wa Mai rahama ne yanã bãwã. 
94. Lalle ne haƙĩƙa Yã lissafe su, kuma ya ƙidãye su, ƙidãya. 
95. Kuma dukan kõwanensu mai jẽ Masa ne a Rãnar Ƙiyãma yanã shi kaɗai ». [ Suratul Maryam ].

 

 

Ma rubuci : Bandar Ahmad