i jin kai litattafan nasarawa suna shaidar cewa Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) manzon Allah ne.


Da sunan Allah mai rahama, mai jin kai

 

litattafan nasarawa suna shaidar cewa Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) manzon Allah ne.

 

Idan kana karanta nassosi masu yawa a cikin littafi mai tsarki wajen nasarawa, wadanda suke kafa hujja da su a kan tabbatar da cewa Isa ( yusu ) Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) dan Allah ne, ba ka samun abin da ke nunin cewa Shi Allah ne, ko kuma dan Allah ne … abin da ke tabbatar da haka shi ne:

Idan ka na karanta wasu nussosi na linjila za ka samu kalimar  (baba na ), ( uba ), ( ma'aifi na) suna  yawan maimaituwa a kan harshen Isa

 

( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ).

Idan ku ka ce: wadannan kalimomi suna tabbatar da cewa Shi Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) dan Allah ne.

Amsa ita ce: Shi littafin linjila idan lalle ya sabko da wadannan lafuzzan, to lalle harshen Magana ya na bada damar ambaton wanda a ke jibintar al amuran shi ( da ); kamar yanda Allah ya ambace ku ( 'ya'ya ) ba tare da kun kasance kamar Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ba.

Ga wasu daga wadannan nassosi:

Allah ya ce wa Isra'il ( annabi Yakub - tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi- ) a cikin littafin futa ( 4/22 ): " ka gaya wa fir'auna: haka ne Ubangiji  Ya fada: Isra'il da na   ne wanda ke matsayi ".

Allah Ya kuma ambaci mataimakan Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) da 'ya'ya; ya zo a cikin linjilar "matta" " ( 5/45 ) : " dan ku kasance 'ya'yan uban ku wanda Yake sama ".

Muna kuma samun kamar haka a cikin linjilar "yuhanna" ( 20/17 ): " sai Isa ya ce da ita: kar ki nemeni, saboda har yanzu ban tafi sama ba wajen uba na, amma ki tafi wajen 'yan uwa na, ki ce musu: lalle ni zan tafi sama wajen uba na wanda ke uban ku,  abin bauta na, kuma abin bautar ku ".

Ka yi tunani game da maganar Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ):  "abin bauta na, kuma abin bautar ku ".

Muna kuma samun kamar haka a cikin linjilar "yuhanna" ( 8/38 ): " Ni ina fadar abin da na gani wajen uba na, ku kuma kun san abin da ku ka gani wajen uban ku ".

Idan kuna kudirin cewa Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) abin bauta ne saboda irin wadannan nassosi, to kenan sauran wadanda irin wadannan nassosi su ka zo a kan su, suma sai ku ce sun cancanci bautar, domin babu banbanci !!!

Abu na biyu: -

Amma abin da ya zo a cikin linjilar "yuhanna" ( 9/14 ): " sai Isa ya ce da shi: ina tare da ku zamani mai tsawo, kuma ba ka san ni ba ya kai Felbis; wanda ya gan Ni lalle ya ga uba, kaka kake cewa: goda mini uba ?".

Ma'anar fadan Shi: " ni da uba na guda ne " shi ne: idan kun bi umarni na, kamar kun bi umarnin Allah ne. kamar yanda dan aike yak e cewa: ni da wanda ya aiko ni guda ne, kuma kamar yanda wanda aka wakiltar  yak e cewa: ni da wanda ya wakiltar da ni duk daya ne; saboda ya aikata abin da wancan zai aikata ne, kuma ya isar da abin da aka aiko Shi da Shi ne,  … kamar haka ne kuma fadar Shi: " wanda ya gan ni, lalle ya ga uba na ". ya na nifin wanda ya ga wadannan ayukka lalle ya ga ayukkan uba na ne ".

Da haka yana bayyana gare mu cewa: " kasancewa daya " a cikin nassosi da su ka gabata ba su nufin cewa wadannan suma Allah ne, Allah ya daukaka daga samun kotankocin Sa, shi kadai ya ke.

Ga bayani a kan haka:

Wannan kalima da Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) Ya firta da ke cewa: " Ni da uba abu guda ne ", ya firta kamar ta game da mataimakan Shi, yayin da ya ce a cikin linjilar "yuhanna" ( 17/20 -23 ): " bana tambaya saboda wadannan kadai, ina tambaya ne saboda wadanda suka yi imani da Ni, domin duka a zama abu guda, kamar yanda kai uba ka ke ciki Na, Ni ma ni ke cikin Ka; domin kowa ya yi imani da cewa Kai ka aiko Ni, lalle kwa Na basu daukakar da Ka bani, domin su kasance daya, kamar yanda mu ke daya; Ni ina cikin su, kai kuma Ka na ciki na; domin su kasance suna magana zuwa ga guda daya ).

Dan haka zama gudan nan abin nifi da shi shi ne: haduwar manufa, da abin so kamar yanda ya ke zahiri a cikin fadar Shi: " domin suma su kasance cikin mu, mu zama daya". Da kuma fadar Shi: " domin su kasance daya, kamar yanda mu ke daya; Ni ina cikin su, kai kuma Ka na ciki na; domin su kasance suna Magana zuwa  ga guda daya ".

Daga cikin ababen da ke nuna mana ingancin wannan: idan mutun ya na da abokai wadanda suke da manufa guda, ta yanda su ke kamnar abu guda, su ke kuma kin abu guda, zai iya cewa: ni da su guda ne.

-  Abu na ukku:  Inda Isa  ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) lalle kamar yanda su ke fada Allah ne da'  ya futo karara ya fadi hakan kamar yanda Ya futo karara Ya ce Shi bawan Allah ne, sai dai bai fadi hakan ba, kuma bai yi kira zuwa ga hakan ba. Kuma litattafai da suka gabace Shi ba su yi nuni ga hakan ba, kamar yanda litattafan alma'jiran Shi ba su yi nuni ga hakan ba, Kuma maganar Jibril( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ga Maryam ko maganar Yahya dan Zakriya ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ba su kunshi hakan ba.

Kuma yana nuni ga ingancin haka abin da ya zo a cikin "linjilar Yuhanna" ( 8/28 ): " sai Isa ( Yusu ) ya ce da su: duk lokacin da ku ka daukaka dan mutun za ku ga cewa Ni ne Shi, kuma za ku ga cewa ba na aikata face abin da Ya umarce Ni, Ni ina fadar abin da Uba Ya ce ne". ga Shi nan Yana tabbatar da cewa Yana fadar abin da Allah Ya umarce Shi ne; wannan kwa yana nuna cewa Shi mutun ne abin halitta, wanda Allah Ya ke yiwa aike; domin manzon Shi ne.

Kuma Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) Yana cewa alma'jiran Shi kamar  yanda ya zo a cikin lijilar Mark ( 9/37) : "daga wanda ke Shi daya, 'ya'yan wanda ke haka suna karba ta da suna na, wanda kwa ya karbe ni, ya karbi wanda Ya aikoni ne ". nan Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi )  yana nuna musu cewa Shi ma'aiki ne, kuma Shi da su duka hanyar su guda ce game da Allah.

Mattah almajirin Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) yana kafa hujja a kan annabcin Ish'iya kamar yanda ya zo a cikin "Ish'iya" ( 1 / 42): " Shine wannan bawa na, ina karfafa Shi da abin zabi na, wanda nai farin ciki da Shi, na sanya ru'hi na tare da Shi domin ya isar da gaskiya ga al ummomi".

Shin muna bukatar wata hujja fiye da haka, Allah Ya bayyana al amarin Shi, ya ambace Shi bawa, Ya kuma bayyana cewa Ya sanya ruhin Shi tare da Shi, domin Ya karfafa Shi da Shi kamar yanda Ya karfafa dukkan manzonni.

Sham'un –shugaban mataimakan Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi )  ya na cewa a cikin littafin "ayukan manzonni" ( 2/22 ): " ya ku mutanen isra'ila, ku saurari wannan maganar: Isa namiji da ga Allhah kamar yanda ya bayyana gare ku da hujjoji, da ayoyi ma su ban mamaki da Allah ya baShi, wannan ya faru ne a cikin ku, kamar yanda ku ka sani ".

Shin akwai wata shaida da ta fi haka, alhali shi ne mafi adalci a cikin alma'jiran Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ); ga shi yana sanar da mu cewa Isa mutun ne da Allah ya aiko, kuma ayoyin da su ka bayyana a hannun Shi da ga Allah ne.

Kuma dauda ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ya ce a cikin zamur na biyu a cikin zabura Yana mai yabo ga Allah ( 8/ 4-5 ): "wanene mutun har da za ka tuna da shi, ko kuma dan Adam  har da za ka rasa shi. 5 kuma Ka sanya shi kasa da mala' iku, ka bashi girma da kyawo".

Ya kuma ce a cikin zamur na biyu ( 2/7-8): "lalle ni ina bada labari ne da abin da Allah ya hakunta, Ya ce da ni: kai da ni ne, yau na samarda kai. 8 Ka tambaye ni zan gadar maka al – ummomi, sa' an nan in saka kasa mulkin ka ce".

FadarShi: " Na samarda kai " yana nuna muna cewa abu ne wanda ke fararre, ba tsoho ba, dukkan fararre kwa abin halitta ne.

Sa' an nan ya karfafa wannan da cewa: " yau na samarda kai"; ya fadi lokacin samar da Shi, kenan gabanin " yau " bai kasance akwai Shi ba.

Kuma cewar Shi: " Ka tambaye ni zan gadar maka al – ummomi " ya nuna muna cewa

Shi mabukaci ne, bai wadata ba daga tambaya.

Aabu na hudu: inda Isa ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) dan Allah ne, ko kuma Allah ne, dan mi almajiren Shi suke kiran Shi "malam" ? kuma dan mi Ya yarda da hakan ?

Diba yanda almajiren Shi su ke kiran Shi kamar yanda ya zo a cikin linjilar Yuhanna ( 4/31 ): " ana haka sai almajiren Shi suka ce da Shi: ya malamin mu Ka ci ".

Ya zo kuma a cikin linjilar mattah ( 22/16 ): " sai suka tura almajiran su zuwa gare Shi

tare da herodosawa suna ma su cewa: ya malam, mun san da cewa kai mai gaskiya ne, kuma ka san hanyar Allah da gaske, kuma ba ka damu da kowa ba, domin ba fuskokin mutane kake dubawa ba ".

kuma ya zo a cikin linjilar Yuhanna ( 3/2 ): " ya zo wajen Yusu da dare ya ce da Shi: ya malam mun san da cewa ka zo daga wajen Allah ne da ka karantar, domin wadannan ayoyi ba bu wanda zai iya zuwa da su face Allah Yana tare da Shi ".

kamar yanda mu ke samu a cikin linjilar Mattah ( 9/ 11-13 ): " lokacin da firisiyawa su ka yi dubi sai su ka ce wa almajiran Shi: saboda mi malamin ku Yake ci tare da talakkawa da ma su sabo ? Lokacin da Yusu Ya ji haka sai Yace da su: ma su lafiya ba sa bukatar  likita, marassa lafiya su ke bukatar likita. 13 ku tafi ku yi karatu, Ni ina son rahama ne ba abin yanka ba, domin ban zo saboda kiran masu biyayya ba, na zo ne domin in kirayi ma su sabo zuwa ga tuba ".

kayi tunanin fadar Shi: " domin ban zo ba saboda kiran masu biyayya, na zo ne domin in kirayi ma su sabo zuwa ga tuba "; ma'ana ya zo ne domin kiran masu sabo, su tuba, bai zo domin a yanka Shi saboda su ba !

zan gama wannan mahawarar da abubuwa biyu:

-  Abu na farko: tana yuwa wani ya yi tambaya: dan mi duk wannan ? kasancewar Isa  ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) dan Allah ne, ko kuma Allah ne, me zai cutar damu ? ko kuma wata maslaha ke cikin hakan ?

Amsa ita ce: babban abin da ke fusatar da Allah shi ne hada shi da wani abin tarayya, domin Shi Allah kamili ne ta ko wane fuska, yayin da shi wannan abin tarayyar da aka hada da Shi nakasasse ne ta ko wane fuska; dan haka mafi girman zalunci shine ka daidaita Allah da wani.

-  Abu na biyu: ni musulmi ne, mai imani da cewa Isa  ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) annabi ne mai girma … daya daga cikin manyan manyan manzonni, Allah Ya halicce Shi ba tare da uba ba, wannan kwa aya ce da ke nuni ga girma da kudurar Allah madaukaki.

Kamar yanda na ke mai imani da cewa: Allah Ya aiko Isa  ( tsira da rahamar Allah ta musamman su tabbata a gare Shi ) ne domin Ya kirayi mutane zuwa ga bautar Allah Shi kadai, wannan kwa shi ne abin da yayi.

Ya zo a cikin linjilar Luka ( 6/ 12 ): " a cikin wadannan raneku Ya fita zuwa ga dutsi domin Ya yi sallah. Ya kuma tafiyar da daren dukkan shi a cikin sallah ".

Lalle ina son alkhairi ga dukkan nasara na duniya …

Dan haka na ke fata za ku karanta wannan ayar mai girma ta Alkura' ni mai tsarki:

« 171. Yã Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafã a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, fãce gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yã jẽfa ta zuwa ga Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabõda haka, ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, « Uku » . Ku hanu ( daga faɗin haka ) yã fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yã tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli ». [ Suratul Al-Nisa ].