Girman manzon Allah


Girman manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi )

 

Shin a ganin ka me ya sa musulmi suke son manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ?

Saboda me suke da kudirin cewa Shi ne shugaban halitta ?

Rayuwar Shi ta sha banban da dukkan rayuwa, kuma ta kebanta da wasu ababe, wadanda suka sanya Shi ma cancanci ga daukar nauyin wannan manzoncin. Sai rayuwar Sa ta kasance babbar mu'u'jiza bayan mu'u'jizar Alkura' ni da aka baShi.

Ya kasance mutun ne, kuma Allah Ya umarce Shi da Ya sanar da mutane hakan; dan kar su dauke Shi a matsayin abin bauta, su kuma ba Shi sifofi na Allah; Ubangijin Shi Ya ce da Shi: { 110. Ka ce: « Nĩ, mutum ne kawai kamarku, anã yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, sabõda haka wanda ya kasance yanã fãtan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kõwa ga bauta wa Ubangijinsa. »}. [ Suratul Al-Kahf ].

Mutun ne mai sifofi na mutane, amma a cikin mutane babu kamar Sa, wajen daukakar Sa da girman sa. Allah bai halacci a cikin 'yan Adam kamar Muhammad dan Abdullah ( tsira da amincin Allah a gare Shi, Shi da annabi Ibrahim, da Musa, da Isa, da dukkan annabawa ).

Kuma yana daga zaluntar Muhammad ( tsira da amincin Allah a gare Shi ), da kuma zalunci ga hakikanin lamari, kiyasta manzo Muhammad ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) da daya daga dubban manya manyan jaruman duniya, wadanda tarihi ya rubuta mana sunayen su; domin sun bar wani babban alama a cikin rayuwar su.

a cikin manya manyan gorzayen nan akwai wanda babba ne wajen kwakwalwa, amma yana da rauni wajen bayani, wani kwa yana da iya Magana amma tunanin shi takaitacce ne, wani kwa ya shahara ne game da jagoranci, amma halayyan sa da dabi'un sa irin na gamagarin mutane ne, ko kuma irin na fajirai ne.

Muhammad ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) Shi kadai ne wanda ya hada dukkan bangarori na girma da daukaka da jaruntaka, saboda wanin Sa ba za ka same shi ba face a kwa wasu bangarori na rauni tare da shi, wadanda kuma ba ya so wani ya san su. Bangarori na shahawar sa, ko wadanda ke da alaka da zamantakewar sa … Muhammad ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) kadai ne ya bayyana dukkan rayuwar sa ga jama'a, sai ta kasance littafi ne a bude, wanda babu shafi rufaffe ko sadara gwogagga a cikin shi; duk wanda yake so zai karanta abin da yake so a ciki.

Shi kadai ne ya umarci sahabben sa da su watsa dukkan abin da ya yi, ko ya fada, ko a kayi a gaban sa bai yi musu ba. Sai suka ruwaito dukkan halayyan sa a cikin halin farin ciki, da halayyan Sa a cikin halin bacin rai.

Kuma matan sa sun ruwaito dukkan rayuwar sa tare da su. Misali Aisha ( Allah kara mata yarda ) ta ruwaito  –yana raye kuma da izinin Sa-  rayuwar Sa da halayyen Sa a cikin gidan Sa; saboda rayuwar Sa dukkan ta shari'a ce. Litattafan tarihi da fikhu suna cike da ababen da suka gabata, ga wanda yake son ya san su tare da dogon bayani.

Sun ruwaita dukkan ababen da suka kasance daga gare Shi, har ma a halin larura, dan haka mun san kaka Yake cin abinci, kaka Yake sanya tufafi, kaka Yake barci, kaka Yake biyan bukatar Shi, kuma kaka Yake tsabtace jikin Shi bayan biyan bukata.

Ku goda mini babba guda wanda ya ce: wannan ita ce rayuta gaba daya, ku isar da ita zuwa ga masoyi da makiyi, idan da abin suka a ciki sai a soka !

Ku goda mini babba guda wanda aka rubuta dukkan tarihin Sa, aka san kome da kome a cikin ta, bayan shekara dubu da dari fudu, kamar Muhammad ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) !

Girma da daukaka suna kasancewa ne, ko dai a wajen halayya da dabi'u da sifofi na mutun, ko kuma game da ayukka manya manya da mutun ya aikata, ko kuma game da tarihi da kufan da mutun ya bari a cikin al ummar shi.

Ko wane babba akwai wani daga cikin ababen da suka gabata wadanda ake kiyasta daukakar shi da su, amma Muhammad ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) daukakar Shi ta kunshi dukkan wadannan ababe ne ! Ya kasance yana da halaye nagari, kamar yanda Yake da kyawawan sifofi da manya manyan ayukka.

Kuma manya kodai suna da girma ne wajen al ummomin su; saboda sun anfane su tare da tsutar da wanin su, kamar jaruman yaki.

Ko kuma suna da girma wajen mutane ne gaba daya; domin sun samar da wani abu mai anfanin jama'a gaba daya: kamar samar da wani magani, ko isa ga wani ilmi da Allah ya boye domin mu awaitar da hankalin mu dan gano shi, …

Amma Muhammad ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) daukakar Shi, ta kasance ta hade duniya gaba daya, kuma ta kunshi dukkan bangarori na daukaka, da maudu' an ta. Kuma Ya kasance mai imani ne da abin da Yake kira gare shi, yayin da, da yawa daga cikin masu kira, suke kira zuwa ga abin da suke sabawa a aikace, kuma suke bayyana abin da suke sabawa a badini, su kan rinjayar da dabi'un su a cikin halin kodai, ko tsoro, ko hushi, ko yunwa, ko bukata, sai su manta dukkan abin da suke kira zuwa gare shi.

Bana magana akan kowa, ina Magana a kai na ne, misali: ina neman kai mutuka yayin da nike bada lacca, ko nike rubutu mai kira ga gaskiya da al khairi da shirya, duk lokaccin da zan daukaka sai dabi'a ta, da son rai na, su yi tasiri a kai na, sai na sake komowa kasa. Wannan kwa mutane suna ganin shi a wajen masu wa'azi da huduba; sai ya kasance ba su tasirantu da wa'azin ba.

Amma manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) bai taba kira ba zuwa ga wata lacca, wadda za ta hada hukunce hukuncen addini ba, bai kuma samar da makaranta wadda ke hada almajirai wasu sa'o'i kayyadaddu ba, kuma bai zauna wani guri musamman dan wa'azi ba, A'a Ya kasance Yana isar da wahayin da aka sauko a gare Shi ne a gida, ko a masallaci, ko a hanya, Yana kuma kira ga kyakyawon aiki, kuma Yana hani daga mummunan aiki a lokacin da aka bukaci hakan. Kuma Yana yin hakan ne da harshen Shi, kamar yanda Yake yin shi a aikace. Lalle halayen Shi sun kasance halayen da Alkura' ni ya yi umarni da su. muna karanta wannan amma ba mu fahintar ma'anar shi; ma'anar shi ita ce: ko wane aiki daga cikin ayukkan Shi, ko wane hali daga cikin halayen Shi, aya ce da ake karantawa, kuma lacca ce da ake badawa, kuma majalasi na karatu; domin dukkan su, suna magana ne da abin da Alkura' ni Ya yi kira a kai.

Ya kasance yana yin sallar nafila da dare har kafafun Shi su tsage, kuma ko da yaushe Yana mai neman gafarar Ubangijin Shi. Da aka ce da Shi: Kana ba kan ka wahala, alhali, an gafarta maka, sai Ya ce: shin ba zan zama ba bawa mai godiya ?

Kuma ya kasance a cikin ayukkan Shi duka yana mai sallah ne; domin dukkan aiki na alkhairi wanda aka nufi Allah da shi, ma'abucin sa tamkar yana cikin sallah ne.

Zan takaita a kan misali guda daya da ke nuna lalle yana kira ga abin da Ya yi imani da riko da shi ne.

Me kuke tsammani inda diyar wani babban mutun za'a tuhumce ta da laifin sata ? shin za'a hukunta ta kamar yanda za'a hukunta diyar talakka wanda ba shi da wani matsayi a cikin jama'a ? ko kwa za ta samu kariya ne saboba matsayin baban ta ? a kuma suturce laifin ta ?

Kamar haka ya faru a zamanin manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ), yayin da wata mata daga kabilar banu makhzum ( gida na uku a wajen girma cikin kuraishawa ), wannan mata ta yi sata, sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) ya yanke hukuncin da Allah ya yi umarni da shi. Sai wasu suka nemi manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) Ya yi mata afuwa, sai hakan ya fusatar da Shi, Ya kuma sanar da su cewa: wannan shi ne ya halakar da wadanda suka gabace mu; domin idan hukunci ya kama a kan wanda bashi da matsayi da galihu, suna zartar da shi, idan kuma ya kama a kan mai matsayi sai su ki zartar da shi.

A nan ne kuma Ya fadi magan nan wadda ta shahara, yayin da Ya ce: "wallahi inda Fadima 'yar manzon Allah za ta yi sata, da Na yanke hannun ta" !

Wannan kuma abu ne a wajen Shi mai sauki; saboda Yana rayuwa da da'awa ne, kuma dan da'awa, son Shi yana daidai da abin da aka aiko zuwa gare Shi ne, dukkan abin da ke sadar da Shi da 'yan uwa, idan ya shiga tsakanin Shi da abin da Yake kira gare shi, to lalle zai yanke shi ne.

Lalle manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) ya kauda kan Shi daga abin da mutane suke rayuwa saboda shi ga al ada, na daga cimaka, da tufafi, ya kuma bar ababen son rai, amma bai kasance ba mai nufin takura wa kan Shi ba, ko neman zama da yunwa – kamar yanda wasu suke yi da sunan zuhudu – kuma ba ya lazimtar tufafin talauci, ya kasance Yana cin kyakyawan abinci idan Ya samu, idan kuma ran Shi ba ya son shi, ba ya cin shi, amma kuma ba ya aibanta shi.

Ba' a taba samun Shi Ya aibanta abinci ba, idan kuma bai samu abincin ba sai ya yi hakuri da yunwa, har ma wani lokacin Ya daura dutsii a cikin shi dan tsananin yunwa. Kuma yana sanya abin da ya samu na tufa, baya lazimtar wata tufa ta musamman, ko wani launi na musamman.

Lalle Ya sanya rawani tare da hula, kamar yanda ya sanya hula ba tare da rawani ba, ko rawani ba tare da hula ba.

Kuma mu san da cewa rawani abu ne wanda mutanen hijaz suke da bukatar shi; domin suna fama da rana mai tsananin gaske, suna kare kanun su da shi daga zafin ranan nan.

A muslunci babu wani dangi na tufafi da aka haramta, face tufafi mai bayyana al aura, ko tufafi na harir ( sulke ) – ga maza -, ko tufafin da aka san mabiya wani addini da shi ( tamkar tufafin da aka san malaman nasara da shi ), ko tufafin na mata ga namiji, ko tufafin maza ga mata, ko tufafin da ke da almubazzaranci a cikin shi.

manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) bai kasance ba mai hana ado da Allah Ya saka wa bayin Sa ba, ko kyawawa daga abin da Allah ya arzutar da bayin Sa ba, kuma ba ya kin su idan ya same su, tare da cewa bai sanya su ba abin neman Shi ba.

Kamar yanda kuma ya bar shahawa ta neman arziki ko suna, kuma kamar yanda ku ka sani kuraishawa sun bijiro maSa dukiya, da mulki, da mata, da dukkan abin da rai ke so a cikin rayuwar duniya a kan ya bar abin da Ya zo da shi na wahayi, amma Ya ki, Yana mai tausaya musu game da halin da suke ciki na bata da dimuwa.

Ya kuma nisanci shahawa ta jinsi ( mata ); amma duk da haka makiya, masu karantar muslunci dan su bata Shi (mustashrikune ) sun tuhumce Shi da cewa: Shi mutun ne mai shahawar mata; domin Ya auri mata tara, wannan kwa ba dan kome ne ba face sun kiyasta Shi da kanun su !

Dan haka su, suna kallon rayuwar manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) kamar yanda suke kallon rayuwar manyan su; dan haka sai suka ce: mutun ne mai yawan shahawar mata, tare da jahiltar wanene manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ), da kuma rishin neman hakikanin rayuwar manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) !!!

Lalle lokacin da mutun ya fi shahawar mata shi ne: daga balaga har zuwa shekara ishrin da biyar ( wannan shi ne lokaci mai hadari, wanda dukkan mai hankali, namiji ko mace, ya kamata ya nisanci abin da zai abkar da shi ga mummunan aiki; kamar kebanta da mata ko da da sunan karatu ne, ko kallon su, ko yawan tunanin su … ).

To, kaka manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) Ya kasance a wannan lokaci ? kuma menene Ya aikata na tir a wannan lokaci ? Lalle kwa ya kasance mai inci ne a cikin garin inci; inda ya so wani abu da babu wani mutun ko wani abu da zai hana Shi yin abin da Yake so, matasa kamar Shi sun durmiya a cikin biyawa rai abin da take so, ba tare da wani addini ko wata doka ta tsawatar musu ba.

Tarihin manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) a bayyane yake ga makiyi kafin masoyi; shin kun ga cewa Shi mai neman biyan bukatar Shi game da mata ne ? ko mai neman biyan bukatar ran Shi ne ?

Lalle ya yi tunani so guda Ya aikata wani abu daga cikin wasanni da warin Shi matasa ke aikatawa, sai Allah Ya jefa mi Shi barci, kuma inda Ya aikata wani abu shin makiyan Shi za su kyale, alhali suna neman abin da za su soke Shi da shi ?

Ya yi aure Yana dan shekara ishrin da biyar; shin Ya auri yariya ne karama kyakyawa, ko kwa Ya auri babbar mace ne mai shekara arbain ? kuma sauran matan Shi, shin mafi yawan su, ba su kasance zawaru ba ? kuma shin bai aure su dan maslaha ba ? kuma lalle Allah Ya halitta maSa fiye da mata hudu, amma kuma sai Ya hana maSa abin da Ya baiwa sauren mazaje; shi ne damar saki.

Wannan kwa tare da sanin cewa karfin Tarawa da mata ba aibi ba ce, hasali ma dai mazakunta ne, kuma abin yabo ne ga namiji, abin zargi shi ne mutun ya maida shi abin tunanin shi ko wane lokaci, ko kuma Ya yi anfani da shi a cikin haram.

Kuma kissar auren Shi da Zainab, wadda makiya ke yawan maimaitawa, ba sai an maida musu martani ba, saboda sun canza hakikanin ta ne da gangan, ko kuma sun yi mata mummunan fahinta ne.

Zainab mace ce mai kyawo, kuma mai dangantaka da manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ), inda Yana son Ya aure ta, da Ya aure ta, kuma wannan shine babban abin begen ta, amma Allah Ya yi niya Ya sa ta zama ma'auni ga abubuwa biyu na gyara a cikin muslunci: na farko ita ce abin godi a kai, na biyun kwa manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) ne.

Abu na farko: Allah Ya so Ya kawar da ji da kai, da kuma ji da fifiko na jahiliya; domin Zainab ( Allah Ya da yarda da ita ) ta kasance mai daukakar asali a cikin kuraishawa, gata kuma da umarnin manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) ta auri zaid dan Harisa ( Allah Ya da yarda da shi da ma'aifin shi ), wanda ke an kama shi wajen yaki ne, kuma manzon Allah Ya dauke shi matsayin da. A dubin wadannan mutane lalle ita ta wuce matsayin ta aure shi; sai ta aure shi ba tare da tana son shi ba, sai kuma rayuwa ta kasance tsakanin su tana cike da sabani da rishin fahintar juna, amma manzon Allah  ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) Ya hana shi ya sake ta, Yana cewa da shi "ka rike matarka, ka ji tsoron Allah" har abu ya kai tsakanin su inda ba'a iya hakuri … sai ya sake ta.

Bayan haka ne jarrabawa ta biyu ta zo, kuma ita ce mafi tsanani, nauyin ta kuma ya kasance a kan manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ); ta zo ne dan ta kawar da al adar danganta yaro ga mutun a matsayin da –kamar yanda yake a jahiliya da farkon muslunci har zuwa wannan lokacin, da kuma bayanin cewa daukan yaro a matsayin da, ba ya haranta auren matar sa. Wannan kwa ya yi matukar nauyi ga manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ); domin kar jama'ar Shi su ce ya auri matar dan Shi. Amma duk da haka dole ya bi umarnin Ubangin Shi na cewa Ya auri Zainab ( Allah Ya da yarda da ita ).

Dan haka hikayar ba kamar yanda suke fadar ta ba ne ba, kuma na kawo ta ne domin wanda bai san ta ba, ya sani.

Karfin jiki shi ne tunkarar kalubalen kayan alatu, karfin zuciya kwa yana tare da nasara ne a kan makiya, kuma akwai wani karfi da ya fi karfin jiki da na zuciya; shine karfin dabi'u da hali na gari, wannan da shi ne mutun zai rinjayi son ran shi.

Wannan kwa mas'ala ce wadda manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) Ya yi bayanin ta a gurare daban daban. Yace: "mai karfi ba shi ne mai karfin kwokowa ba, mai karfi shi ne mai iya rike kan Shi idan ya yi hushi".

Wannan kwa gaskiya ne da za ku iya gani a tare da kanun ku; idan karfin da ka ke sanyawa wajen kwokowa da wani ka kaddara shi da daraja daya, to karfin da za ka bukata wajen rinjayar fushin ka, da maido da zuciyar ka ga yanda take ya fi wancan karfin so dari. Ka jarraba mutun wanda fushi ya rife ma idanu, ka yi kokarin maido da shi ga hayyacin shi, da rokon shi, ka ga shin a cikin dubu goma za ka samu mutun guda wanda zai karba maka  ?

Ka kaddara cewa wani ya kashe maka wani babban masoyi, mai girma a gareka, sa' an nan ya zo yana mai amsa da'awar ka, shin za ka manta hawayen ka da ka zubar a kan dan uwan ka, masoyin ka ? shin za ka iya yin afuwa ?

Lalle, to, manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) Ya yi afuwa ga Wahshi ( Allah Ya da yarda da shi ) wanda ya kashe ka'un shi Hamza( Allah Ya da yarda da shi ), yayin da ya muslunta; abin da ya nema a wajen shi, shi ne kawai kar ya bari ya rika ganin fuskar shi, sai ya kasance ya na rife huskar shi.

Hindu matar Abu sufyan ( Allah Ya da yarda da su ), wadda kiyyayar ta ga manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ), ta kai inda har ta aikata abin da mace ba za ta iya aikatawa ba, kai dan adam ma zai yi wuya ya aikata shi; ta tsaga kirjin Hamza    ( Allah Ya da yarda dashi ), ta futar da zuciyar shi, ta kuma ci zuciyar ! amma duk da haka manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) ya yi mata afuwa, Ya karbi mubaya'ar ta, kuma ya yarda da musluncin ta.

Ga kuma mutanen Taif, wadanda kun san labarin su tare da manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ), yayin da suka muslunta Ya yi mu su afuwa.

Ga kuma babban abin da tarihi ba zai taba mantawa ba; mutanen Makkah wadanda suka gana miShi, Shi da sahabban Shi mummunar azaba, suka cutar da su game da akidar su, da kuma jikunkunan su, suka bata Shi da kazamtar ma'aifa alhali yana cikin sujada, sukai ta muzguna musu a tsawan shekara goma sha uku, suka kuma yake Shi, suka yanka wasu daga cikin sahaban Shi … yayin da Ya samu nasara a kan su, mi ya ce da su ? me kuke tsammani zai aikata da ku ?

Lalle suna tune da ababen da suka miShi, shi da sahabban Shi, kuma sun san abin da suka cancanta, amma duk da haka suna kuma tuna kyawawa halaye na manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ); dan haka sai suka bada amsar cewa: 'kai dan uwa ne mai karamci, kuma dan dan uwa ne mai karamci".

Bayan haka sai suka jirayi amsa wadda za ta iya kaiwa ga kisan su gaba daya, amma hukuncin manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) da amsar Shi ta kasance abun mamaki wanda da tarihi ya rubuta har zuwa tashin kiyama, wanda kuma ba' a taba samun irin shi ba; Ya ce da su: "ku je, ku sakakku ne".

Rishin jin dadi na shine kasancewar na gabatar muku da wannan kissa a takaice; domin na so a ce: maudu'in gaba daya akan wannan kissar ne; yanda zan samu damar yin bayani fiye da haka.

Kuma ina mamakin me ya sanya mawallafan tarihin manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) suke Ambato ababe da ba su inganta ba game da mu'u'jizozin Shi, alhali kwa rayuwar Shi cike take da mu'u'jizozi !

Shin mu'u'jiza ba ita ce: abin da mutane ba za su iya kawowa ba ?

Gaskiyar Shi, da amanar Shi mu'u'jiza ne. Ba zan koro muku da yawa daga wadannan mu'u'jizozin ba, zan koro misali guda daya ne, na karanta shi so da yawa, amma hankali na bai zo gare shi ba sai a karshe, na same shi abin mamaki, lalle rayuwar Shi tana cike da abin mamaki !

Kowa ya san lokacin da zai yi hijira, Ya bar Ali ( Allah ya yarda da shi ); domin ya maida amanonin mutanen kuraish zuwa ga masu su, shin kun yi tunani a kan kissar wadannan amanoni ?

Zai mayar da su ga kafiran kuraish ba musulmi ba ! domin dukkan musulmi sun yi hijira, saboda Shi ne na karshe a wajen yin hijira, wannan kwa shi ne hali na shugaba na gaske.

Kissar ita ce: kuraishawa duk da adawar da ke sakanin su da manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ), ba su samu wani da za su lamincewa game da ajiyar su wanin manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) ba. Kaka za ka kasance cikin yaki da mutun kuma ya kasance shi ka ke ba ajiyar kayan ka ?! shin kun taba jin haka ? kaka mutunan nan zai mayar da ita idan bai kasance mai amana da gaskiya ba?

To, lalle haka manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) Ya kasance !

Kuma ranar yakin Badar ya na tsara safun sojojin Shi, a hannun Shi akwai wata sanda karama, sai ya samu sawad dan gaziya ya futa kadan daga safu, sai ya dan zungure shi da wannan sanda, ya ce da shi: "daidaita ya kai Sawad", sai ya ce: Ka ji mini ciwo, ya manzon Allah, kai kwa an aiko ka ne dan adalci. Ku diba, a ce: shugaban sojoji, wani a cikin  sojoji ya ce da shi: ka zungure ni, kaka zai kasance ?

zai ladabtar da shi ne ? ko kuma zai kyale shi ne ? ko kuma kaka zai kasance ?

Amma manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) cewa ya yi da shi: zo ka rama kamar yanda na yi maka !!!

Haka manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) ya kasance, rayuwar shi dukkan ta mu'u'jiza ce, domin dukkan ma su girma sun kasa zuwa da rayuwa irin taShi. Lalle Ya kasance mai girma ne ta ko wace fuska, ya kasance jarimi wanda sahabban Shi suke neman kariya da Shi idan yaki ya bace, duk da haka kuma Ya kasance mai sabko da kan Shi ne ga talakka da miskini da tsofuwa …

- A cikin tabbatar da gaskiya, da isar da sako zuwa ga halittu; domin Ya ma isar da ayoyin da suke nuna kuskuren Shi a cikin wasu ababe … a cikin cika alkawali, da tsayuwa kan magana guda duk yanda zai kasance.

- A cikin zamantakewar Shi; shi ne ya sunnanta yanda ake cin abinci, ya kuma zo da ka'idodin tsabta. Yana rayuwa kamar yanda sauran mutane ke rayuwa, yana shawartar su, yana zama tare da sahabban Shi ba tare da Ya banbanta kan Shi ba, har ma idan wanda bai san Shi ba ya zo yana neman Shi, zai ce: wanene Muhammad a cikin ku ?

- A cikin tafiyar da rayuwar Shi a gidan Shi tare da iyalin Shi, cikin wasan Shi wanda ba ya karya a ciki, cikin rishin girman kan Shi, da rishin son sarautar Shi.

- Ya hana sahabban Shi su tashi idan sun gan Shi dan girmamawa, kuma ya taya matan Shi aiki, yana kuma dunke takalmin Shi …

- Kuma Ya rayu rayuwa ta talauci ba dan baya iya samun dukiya ba, amma ya zabi gidan lahira, dan haka gidajen matan Shi bai wuce meter ishrin da biyar ba.

Dakin Aisha ya kasance na laka ne, ba ya isa yanda zata mike kafafunta kuma Ya samu gurin sallah; dan haka idan Yana sallah lokacin da zai yi sujada sai ta tattare kafafunta ! kuma sai ayi kwana arba'in ba tare da an hura wuda a gidan Shi ba, sai dai a ci dabino a kuma sha ruwa.

Wannan shi ne abincin gidan manzon Allah ( tsira da amincin Allah a gare Shi ) !

- A cikin bayani da fasahar Shi, shi ne fiyayyan wanda ya yi magana.

Wannan duka mu'u'jizozin Shi ne ( tsira da amincin Allah a gare Shi ), kuma a cikin su akwai kwararan dalilai a kan cewa Allah bai sanya Shi cikamakin annabawa har sai da Ya shirya Shi ga hakan, a game da halayen Shi da dabi'un Shi ba Shi da kwatankwaci ( tsira da amincin Allah a gare Shi ); Allah kuma Shi Ya san inda Yake saka manzoncin Shi.

Marubuci: Sheik Ali dandawi ( Allah rahamce shi ).

A cikin littafin shi mai suna: sanarwa a dunkule game da addinin muslunci.