Hikma  a cikin awaitar da haddin da shari'ar muslunci ya zo da su


Abin da dukkan ma su hankali suka hadu a kai shine cewa: ukubobi da ladabtarwa ba su tsaida ta'addanci, ko rage su muddun dai wadannan ukubobin ba su kasance ma su tsanani ga 'yan ta'adda ba. Dan haka muslunci ya zo da haddi da ukubobi ma su tsawatarwa domin samarda koncin hankali ga dan Adam, da kuma kiyaye mutane daga barna; saboda jama'ar da ta'addanci ya yadu a cikin ta jama'a ce abin yiwa barazana da halaka da rugujewa, domin kwa wannan jama'ar ta rasa ginshikai na musamman na tabbatar ko wace jama'a.

Yana daga ababen da muslunci ya kebanta da su; kasancewar Shi mai hadewa ne; ba ya diba bangaren ukuba kadai, ba tare da kawo magani ba; hasali ma ukuba ita ce mataki na karshe a cikin muslunci …

 

Hanya ta Ubangiji tana kokarin hana hanyoyin da ke sune sababin ta'addanci ne da farko; domin kad su abku.

Sai shari'ar muslunci ta zo domin ta samar da jama'a mai tsoron Allah, da kaunar rahamar Shi, tare da kyautata aiki; saboda ko wane mutun a cikin wannan jama'ar yana da kudurin cewa zai hadu da Allah ubangijin Shi domin ya sakauta mishi a kan abin da ya aikata a zaman shin na duniya; tsoron dan sanda ko kuma kotu ba ya isa wajen hana ta'addanci, dole sai an samu wani abu daban da zai tsawatar da mutane ga barin ta'addancin; saboda kwa akwai cin hanci, da daukar lawyoyi kwararru, da shaidu na zur, … wadanda su ke kare dan ta'adda a kan karya, wajen alkali ko dan sanda; wannan kwa yana sanya shi ba ya tsoron wata ukuba domin zai iya kauce wa dokar.

 

Yayin da zamu samu doka ta mahalitti tana hada dukkan wadannan bangarorin; kudurin cewa akwai ranar lahira shine babban abin da ke hani ga aikata jarima da ta'addanci, kuma ya isa ya sanya mutun yana jin cewa akwai nauyin ta'adancin da ya aikata, ko da kwa an dauraye shi a gurin alkali …

 

Sa' an nan abu na biyu: muslunci yana karfafa alaka tsakanin mutun da ubangijin shi, ta hanyar bauta da ke tsarkake zuciyar shi, da ke kuma tsabtace halayen shi … wannan alakar mai karfi tsakanin bawa da ubabgijin shi tana aifar da kumyar Allah a cikin zuciya, da kuma so da tsoron Allah da ke sanya mutun ya hanu daga abin da ke husatar da Allah.

 

Abu na ukku: muslunci yana karfafa ababen da ke sanya so da rahama tsakanin muminai, kuma yana karfafa dangantaka tsakanin su; dan haka ya umarci musulmi idan ya hadu da dan uwan shi musulmi ya mishi sallama yana mai cewa: kubuta da rahamar Allah su tabbata a gare ka, tare da albarkar shi. Sa' an nan ya mika mishi hannun shi, ya kuma yi mishi murmishi, ya kuma yi Magana da shi da kyawawan lafuzza … ya kuma rahamci karami, tare da girmama babba …

 

Abu na hudu: muslunci rahama ne ga mutane; dan haka za ka same shi ya sanyawa talakkawa da mabukata wani kaso a cikin dukiyoyin mawadata; ya umarci ma su dukiya da su futar da zakka; zakkan nan kwa wani kasone  dan kankane, wanda ba ya tsutar da mawadaci, tare da cewa zai anfani mabukaci idan aka bashi shi; wannan kwa yana sanya mabukaci ba zai yi hasadar mawadaci ba, kuma ba zai samu kin shi a cikin zuciyar shi ba, kuma yana hana shi abkawa cikin jarima da ta'addanci .., hasali ma Manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya sanya taimakon wanda bai iya aikin shi ba cikin aikinnashi sadaka ne.

Abu na biyar: muslunci ya kula da iyali da dukkan abin da ke karfafa dangantaka tsakanin su, saboda nan ne marenar yaro; domin ya taso da halaye na gari.

 

Abu na sida: muslunci yana tarbiyantar da mutun a kan tarbiya da ke da anfani ga jama'ar shi bayan ta anfane shi, shi da kan shi … sai ya sanya daga cikin ladubban huta daga gida mutun ya ce: Allah ina neman tsarin Ka daga na yi tuntube, ko a sakani na yi tuntube, ko na bace, ko a batar da ni, ko na yi zalunci, ko a zalunce ni,  ko na yi jahilci, ko a yi jahilci a kai na .. idan ya kasance haka me ya sa mutun zai yi sata, ko ya yi ta'addanci na kisa ko raunatarwa ?!

Abu na bakwai: muslunci tsakatsakiya ne tsakanin ababe masu karo da junann su; abin da ya sa mutane da yawa imani da Shi, muslunci ba ya diba bangaren tausayi da rahama kadai, kuma ba ya diba bangaren tsanani da ukuba kadai, a'a yana diba bangarorin guda biyu ne kuma ya tsaya tsakiyar su ba tare da wani bangare ya rinjayi wani ba!

Abu na takwas: muslunci yana haramta dalilen kiyayya da adawa tsakanin mutane; ya haramta izgili, da yi da mutun, da annamimanci, da girman kai … kuma ya haramta zagi da kaskantar da wani … kuma ya samar da ukubobi ma su tsawatar ga dan ta'adda domin su hana shi tunanin ta'addancin, yayin da kuma ita wannan ukubar take kontar da hankalin shi wanda aka zalunta tare da faranta ran shi.

Daga cikin ukubobin nan akwai ukubar kisasi ( kisan wanda ya yi kisa, ko fudda hakorin wanda ya fudda hakorin wani … ).

 

Kisasi yana da hikmomi masu yawa, daga cikin su:

1 – tsawatar da zukata ga barin ta'adi.

2 – tafiyar da hushin wanda aka yi wa ta'adin ko kuma magadan shi.

3 – kiyaye rayuwa da gabbai.

4 – tsarkake zunubin wanda ya yi kisan.

5 – adalci tsakanin mai kisa da wanda aka kashe.

6 – rayuwa ga jinsin dan adam.

Allah madaukaki ya fadi wadannan fa'idodin da wasun su a dunkule a cikin fadar Shi: " 179. Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma'abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa ", Suratul Al-Baqarah 179.

 

imba dan kisasi ba da duniya ta bace, kuma mutane sun halaka junan su.

Abin da ke tabbatar da haka .. sakamakon abkuwar ta'addanci da ke da kwai  tsakanin kasashen da ke aiki da kisasi da wadanda ba sa aiki da shi:

Lalle yawan ta'addanci da kisa yafi nesa ba kusa ba a cikin kasashe wadanda ba sa aiki da shari'ar muslunci.

Shari'ar kisasi a muslunci ta zo ne dan ta tabbatar da cewa mutane daidai suke .. daidai wajen jinin su, wajen gabban su, hakori daidai ya ke da hakori, kunne daidai yake da kunne …

 

Allah yana cewa a cikin Al kura' ni: " 45. Kuma Mun rubuta a kansu, a cikinta cewa, lalle ( anã kashe ) rai sabõda rai, kuma ( anã ɗebe ) idõ sabõda idõ, kuma ( ana katse ) hanci sabõda hanci, kuma kunne sabõda kunne kuma haƙori sabõda haƙõri kuma a raunuka a yi sakayya. To, wanda ya yi sadaka da shi, to, shi kaffãra ce a gare shi. Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzãlumai." Suratul Al-Ma'idah.

Mutane game da hukuncin Allah daidai suke duk yanda dangantakar su da matsayin su .. suka sha banban, ba bu banbanci tsakanin mai mulki da talakka .. kowa da kowa daidai suke game da hukuncin Allah.

Wannan kwa shine misali na adalci mai daukaka wanda ya kai matuka wajen girmama dan adam, tare da tabbatar mishi hakkin shin a rayuwa, yana mai koncin hankali game da ran shi , da jinin shi, da dukiyar shi, da mutuncin shi .. dan ya samu damar aiki da bunkasa rayuwa .. domin dukkan al – ummah ta kasance tana rayuwa a koncin hankali.

Kuma muslunci ya tabbatar da wannan adalcin tun fiye da shekaru 1430, yayin da dokoki da dan adam ya zo da su, suka kasance ba su kai ga wani daga cikin wannan adalcinba imba nan kusa ba.

Tare da wannan duka muslunci ya bada dammar afuwa; domin yana karfafa gyuwar majibintan wanda aka kashe da su yi afuwa ga wanda ya kashe dan uwan su, kuma ya rataya wannan da lada mai yawa a lahira, tare da amsar diya bayan sun yarda da afuwar. Kuma ya nemi 'yan uwan shi wanda ya yi kisan da su taimakawa juna wajen biyan wannan diyar .. amma idan 'yan uwan wanda aka kashe suka ki yarda da afuwa, to dole ne alkali ya zartar da kisasi.

Lalle musulmi sun yi imani da cewa Allah shine Ubangijin su; kuma dan haka suka yarda da dukkan hukunce hukuncen Shi; zaka samu shi wanda ya aikata ta'addancin ya yarda da hukuncin Allah a kan shi, saboda ya tabbatar da cewa ukubar Allah a lahira ba ta da makawa idan ba'a zartar da ita a nan duniya ba.

 

Ta wata huska kwa: dukkan wanda ya shaida zartar da ukuba, ko ya ji labarin ta, ko kuma ya karanta labarin zaka same shi yana mai addu'a ga wannan wanda a kayi wa ukubar, kuma yana nema mishi afuwa da rahamar Allah .. kuma za su mishi wanka, su saka mishi likkafani, kuma su bunne shi a makabartar musulmi.

 

Kuma musulmi suna kula da iyalin shi wannan wanda aka yi wa kisasi, kuma ba sa muzguna musu .. saboda muslumci addinin rayuwa ne .. addinin rahama ne.

 

Saboda haka ne wadanda ba sa hukunci da abin da Allah Ya hakunta suka cancanci a sifanta su da zalunci … Allah ya ce a karshen ayar kisasi, da ke cikin surat al – ma'ida: " Kuma wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waɗannan su ne azzãlumai. "