auran fiye da mace guda a muslunci


 

auran fiye da mace guda a muslunci

 

haliccin shi – ka'idodin shi – hikma a cikin shi

 

aure a muslunci alaka ce mai daukaka da daraja, alaka ce mai tsabta da Alkura' ni da sunna su ka yi wasi'ci mai karfi da shi, musamman ma ga matasa.

Duk wata alaka ta jinsi wajan aure alaka ce haramtatta a muslunci, kuma zina ne da  muslunci ya tanadi ukuba a kai, mummunar alaka ce da musulmi suke ki.

A wani bangaren kwa muslunci ya bada damar auran fiye da mace guda, kamar yanda ya bada damar saki idan ba'a samu fahimtar juna tsakanin ma aurata ba, ba'a tilasawa mutun zama da wani; namiji yanada damar saki, kamar yanda mace ke da damar neman saki wajen alkali a kwotu. Wannan kwa dan kowa daga cikin su ya je ya yi wata rayuwar tare da wani abokin zama da yake ganin ya fi masa.

 

Auran fiye da mace guda kwa abu ne da musulmi suka karba da hannu biyu; domin shari'a ce daga Ubangijin talikkai, wanda ke sanya kome a gurin da ya datse; shine ya san abin da ke anfanin su da abin da ke anfanin rayuwar su, ya kuma san bayin Sa fiye da yanda suka san kanun su, dan haka dukkan ababen da Ya shar'anta rahama ne ga bayi. Allah madaukaki Yana cewa: { 14. Ashe, wanda Ya yi halitta bã zai iya saninta ba, alhãli kuwa shi Mai tausasãwa ne, kuma Mai labartawa?} [Suratul Al-Mulk]. Dan haka ne duk abin da muslunci ya shar'anta yake da matsayi da karbuwa a cikin zukatan musulmi.

Amma matsayin wadanda ba musulmi ba game da wannan hukunci dayan biyu ne: imma dai wanda ya jahilce shi ( bai san abin da ya kunsa ba, da ka'idodin shi, da maslahar da ke cikin shi ). Ko kuma mai taurin kai wanda hasada ya makantar da shi; wanda ya riki wannan mas'alar domin yakar muslunci gaba daya, tare da bada sura marar kyau game da rayuwar mace karkashin wannan hukunccin da muslunci ya tanada, wannan kwa dan a karshe ya je ga cewa muslunci bai kamata ba ya kasance tsari na rayuwa a zamani na ilmi da tsigaba da inci !

 

Zamu kaddamar da auran fiye da mace guda a mataki biyu; domin bayani a kan gaskiyar lamarin shi:

1 – halaccin shi tare da bayanin ka'idodin shi.

2 – hikmar da ke cikin shi, tare da maslahar da ta sa aka shar'anta shi.

Muslunci ya zo ya samu mutun guda yana auran fiye da mata goma; kamar yanda imam malik ya ruwaito cewa: manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya ce da Gailan dan umayya – lokacin da ya muslunta, alhali yana da mata goma -: "ka zabi hudu a cikin su, ka saki sauran".

Kuma ibn majaha ya ruwaito daga Alharis dan kays yana cewa: "na muslunta ina da mata takwas, sai na gaya wa manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ), sai Ya ce da ni: ka zabi hudu daga cikin su".

Kenan mun ga cewa halitta mata hudu sanya haddi ga abin da suka kasance suna yi na auran mata ba tare adadi ba.

Allah madaukaki Yana cewa: { 3. Kuma idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba a cikin marãyu, to, ( akwai yadda zã a yi ) ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu- biyu, da uku- uku, da huɗu- huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, ( ku auri ) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba } [ Suratul Al-Nisa ].

Wannan hukuncin yana tare da miza guda biyu:

1 – auran fiye da mace guda, tare da haramta auran fiye da hudu.

2 – wannan damar tana tare da sharadin iko wajen adalci tsakanin su ne, wanda baya iya yin adalci, to wajibi ne a kan shi ya takaita a kan mace guda.

Za mu ga a cikin tafsirin kurdubi game da fassarar wannan ayar yana cewa: "fadar Allah: { to, ( ku auri ) guda } ya yi hani ga Karin aure wanda babu adalci tare da shi a wajen raba kwana da kyakyawan zamantakewa. Wannan kuma dalili ne a kan wajabcin  adalci".

Ya kuma zo a cikin tafsirin ibn kasir abin da nassin shi, shi ne: "fadar Allah: { Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, ( ku auri ) guda ko kuwa abin da hannayen ku na dama suka mallaka } abin nifi shi ne: idan kun ji tsoron rishin adalci tsakanin matan, to sai ku takaita a kan mace guda".

A cikin tafsirin shaukani kuma ya zo cewa: ""fadar Allah: { Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, ( ku auri ) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka } ma'ana: idan kun ji tsoron rishin adalci tsakanin mata a wajen rabo da abin da ya yi kama da haka, to sai ku auri guda daya; a cikin haka kwa akwai hanin kara aure ga wanda ya ji tsoran rishin adalci tsakanin matan.

Ya kuma zo a cikin tafsirin al bagawi: "fadar Allah: { Sa'an nan idan kun ji tsõro } ma'ana: ku ka ji tsoro, ko ku ka san cewa { bã zã ku yi ãdalci ba } tsakanin matan hudu { to, ( ku auri ) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka }.

Sheik Sa'adi ya ce a cikin tafsirin shi: "to lalle ba'a halitta masa haka ba sai idan ya yarda da kan sa a kan ba zai yi zalunci ba, kuma ya tabbatar da cewa zai iya basu hakkokin su, idan ya ji tsoron gazawa a cikin daya daga ababen da suka gabata sai ya takaita a kan mace guda".

Kuma wajabcin adalci shi ne abin da malaman muslunci can da, da yanzu suke yin fatawa da shi.

Daga cikin fatawowin nan akwai fatawar Muhammad ibn Ibrahim, yayin da ya bada amsa ga tambaya da ta zo mishi daga indiya. Wannan ita ce tambayar: me nene hukuncin auran mace ta biyu bayan yana da mace guda ?

Sai ya bada amsa kamar haka: "mutun yana da dama a kan ya kara aure a kan matar shi … amma yana zama wajibi a kan shi ya yi adalci tsakanin matan, kuma kar ya karkata zuwa ga wata daga cikin su wajen rabo da ciyarwa da tufatarwa da abin da ya yi kama da haka, hasali ma zai kebewa ko wace daya da cikin su dare da yini da zai kasance a wajen ta, kuma ya kasance wajen ta, kamar yanda ya ke a wajen gudar".

Wannan fatawar ta kunshi bayani a kan hukuncin kara aure tare da wajabtar da adalci, kuma ta bayyana ma'anar adalcin.

Adalcin da muslunci ya shardanta shi ne: adalci a cikin mu'amala, da ciyarwa, da kwana; manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya yi bayani game da haka yayin da ya ce: "wanda yake da mace biyu, ya karkata zuwa wajen guda zai zo ranar kiyama sharen shi yana jan kasa".

Amma adalci a wajen so na zuciya da abin da ya yi kama da haka Allah bai wajabtar da shi ba a kan namiji; domin abu ne wanda mutun ba ya mallakar shi.

Babban misali na adalci shine manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ), wanda duk duniya ba' a taba samun irin adalcin shi ba; kuma duk da haka a cikin matan Shi ya fi son Aisha ( Allah ya dada yarda da ita ), wannan kwa tare da cewa Shine fiyayyen wanda ya yi adalci tsakanin matan Shi. Kuma ya kasance yana cewa: "Allah wannan shine adalci na game da abin da nike da iko a kai, kar ka kamani da abin da ba ni da iko a kai"; adalcin da ba Shi da iko a kai shine son zuciya da abin da ya yi kama da haka; shine kuma abin nifi a cikin fadar Allah ma daukaki : { 129. Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai } [ Suratul Al-Nisa ].

Wannan shi ne bangaren guda na mas'alar: cewa muslunci an rigaye shi da auran fiye da mace guda kamar yanda ya zo a cikin bukhari game da kissar annabi Sulaiman da Ya konta da fiye da mace dari a dare guda. Dan haka muslunci ya zo dan ya tsara shi, tare da sanya haddi a cikin shi, da kuma shardanta adalci.

Amma bangare na biyu game da mas'alar shi ne: menene hikmar shar'anta shi ?

Amsar tambayar wannan tana bayyana ne idan muka tuna cewa muslunci tsarin rayuwa ne ga mutun, tsari ne wanda ya yi daidai halin dan Adam da larurorin shi, kuma ya na daidai da canje canjen rayuwar shi a cikin ko wane guri da ko wane zamani.

Shi ba tsari ba ne ba da ke kunshe da ababe wadanda ba'a iya awaitar da su ba, tsari ne wanda ke tafiya daidai da daidai tare da dabi'ar dan Adam.

Tsari ne da ke kula da halaye na gari game da dan Adam, tare da tsabtace rayuwar dan adam, bai yarda da gina rayuwa a kan dukiya ba tare da barin halayya da suka kamata ba. Dan haka ya na gina rayuwa ce wadda ke kare halayya na gari, abin yabo daga dukkan masu hankali, wannan kwa ba tare da ya dora ma mutane wani babban nauyi ba.

Idan muka kasance tare da wadannan ababe da suka gabata game da ababen da muslunci ya kebanta da su, to me zamu gane game da maudu'in mu ?

Abu na farko da zamu gani game da maudu'in mu shi ne: idan muka diba tarihi zamu ga cewa akwai lokutta masu yawa da adadin mata ya haura na maza saboda dalilai daban daban, amma har yanzu ba'a samu cewa ba mata sun lunka maza so hudu ba.

Kidaya  da ake gudanarwa na nuni ga cewa adadin mata ya fi na maza dalilin kasancewar an fi aifuwar matan, kuma sabo da mutuwar maza – da ikon Allah ta fi yawa – maza su ke zuwa yaki wanda ke tafiyar da adadi mai yawa daga cikin su, kuma maza sun fi yawan huskantar hadurra, su ke zuwa neman abinci fiye da mata, kuma suna yin kome domin su samu abin da su da iyalen su za su ci, wannan kuma abu ne da ke bujarar da su ga cutoti. Wannan a zamanin da mata suke zama a gidajen su.

Abin da ke kara matsalar kwa shi ne: karancin abin hannu, da matsalar tattalin arziki da ke hana wasu mazan yin aure.

Kamar yanda wasu suke jinkirta aure har zuwa wani lokaci dan su samu kyautata tattalin arzikin su zuwa ga halin da za su iya rike iyalin na su; wannan kwa zai kawo cikas ga 'yan mata ma su son yin aure tun suna matasa.

Kaka za mu magance wannan matsalar da ke maimaituwa sabo da dalilai daban daban ?

Zamu kyale ta ne ba tare da nema mata magani ba ? ko kwa dole ne mu nemi magance shi ?

Amsa ita ce: dukkan mai hankali da dukkan mai kishin jinsin dan Adam zai ce: dole ne a nemo wa wannan matsalar magani.

Kenan dole sai an samar da wani tsari, wanda za'a awaitar.

A sakamakon hakan zamu samu kan mu tsakanin zabi ukku:

1 – kowa daga cikin maza ya auri mace daya, sauran matan kuma su zamna ba tare da aure ba a cikin rayuwar su !

2 – ko wane namiji ya auri mace guda aure na halal, sa'an nan ya kasance yana da wasu mata da yake hulda da su a boye !

3 – ya kasance an baiwa ko wane namiji damar ya kara aure a bayyane, yanda ko wace daya daga cikin matan ta san cewa mijinta yana da wata mace da ke tare da shi a kan ka'ida, ba abokiya ba a boye !

- Zabi na farko ya saba wa dabi'ar dan adam, kuma abu ne wanda ba zai taba yuwu ba, ko da kwa masu yaudarar mata sun ce: mace zata iya shagaltar da kan ta da aiki, domin ta manta da menene namiji. Mas'alar ta wuce yanda wadannan da ke ganin al amurra a sama sama suke zato, wadanda suka jahilci hakikanin dan adam da dabi'un shi. Duban ayukka duk yanda suke da tsanani ba za su iya mantar da mace namiji ba, kamar yanda aiki komin tsananin shi ba zai iya mantar da namiji mace ba … wannan kwa ta bangaren bukatu na jiki na bukatuwa zuwa ga saduwa,  da bangaren bukatu na rai da hankali da Allah Ya saka a cikin dan adam, tamkar mazauni da abokin kore kewa. Namiji ya na aiki ya na wahala, amma duk da haka dole sai ya nemi mace abokiyar zama, haka ma mace; domin asalin su guda ne.

- Zabi na biyu kwa ya saba wa zabin muslunci mai tsabta, domin yana tozartar da mace, da cin mutuncinta.

- zabi na ukku: shi ne na shari'ar da ke sanya kome a gurin da ya kamata, mai karrama mace da ajie ta a matsayin da ya kamace ta, wanda bai yarda da fasikanci ba, ya ke kuma neman ko da yaushe a daga matsayin dan adam kololuwa, tare da tsarkake shi daga dukkan abin da zai zubda mutuncin shi, ko zai kai shi ga damuwa. Wannan kwa ba tare da wahaltar da shi ba, ko kallafa masa abin da ba zai iya ba.

Idan muslunci ya litasawa mace ta yarda da auran wata mace a kan ta, to bai haramta mata ta kasance shugaba a cikin gidanta ba; domin a muslunci yana daga hakkokin mace kar a hada ta da wata a cikin gida guda. Kuma wata daga cikin matan ba ta da iko a kan sauran.

Kuma wasu malamai suna ganin cewa mace tana da damar shardantawa mijin ta kafin aure cewa ba zai auri wata a kan ta ba, idan kuma ya saba sharadin zata iya neman rabuwa. Idan kuma ba ta samu daman shardanta hakan ba, sai kuma mijin ta ya kasa wajen kula da ita, ko wajen bata wani hakki da ta ke cancanta, ko ya cutar da ita, tana da hakin neman rabuwa da shi.

Ba mu da sabani a kan cewa kasancewar mace tare da wata a karkashin namiji guda zai rage mata jin dadi da walwala da take bege a cikin rayuwar ta, amma cutarwar da ke a cikin hakan bai kai cutuwar da za ta fuskanta ba idan ta kasance ba tare da miji ba. Wadda ke kin mijin ta ya auri wata mace, zai iya kasancewa ta so ita ta kasance karkashin wani namiji wanda yake da wata matar, idan ta rabu da mijinta ko ya mutu !

"sa'an nan muna gani a cikin mutane, can da, da yanzu, haka ma a gaba har abada, hakika da babu wanda zai iya inkarin ta; ita ce: namiji zai iya kaiwa shekara saba'in yana aifuwa, tare da cewa mace aifuwarta tana tsayawa ne bayan shekara arba'in ko arbain da biyar, ko kuma mafi yawa hamsin, to wannan tazara ta shekaru ishrin da namiji yake da damar aifuwa a cikin su, kaka zai yi da su ? babu shakka cewa a rayuwa namiji da mace suna haduwa ne dan ci gaban nau'in dan adam a ban kasa, da yawantar da zuriya; domin a gina duniyar kamar yanda Allah Ya yi umarni. Idan muka ce namiji ya tsaida aifuwa da zaran matar shi ta kare aifuwa, to lalle hakan zai sha karo da wannan manufar.

Dan haka za mu ga cewa hukuncin muslunci shi ne ya yi daidai da wannan manufa, kuma shi ne ya yi daidai da yanda Allah ya halitti bayin sa.

Wannan muna magana game da jama'a ta mutane ne, can da ko yanzu, ba muna magane ne ba game da daidaikun mutane ba, domin wannan zabi ne da muslunci ya baiwa mutun, ba wai ya tilasta shi a kai ba, dama ce da aka bashi lokacin bukata. Kuma ita wannan dama ta yi daidai da yanda Allah Ya halicci bayin shi, kuma ba ta yi karo ba da tsarin shari'ar da mahalitti ya sahar'anta ba, duk da cewa wannan galibi ya na shan karo da shari'ar da 'yan adam suka kirkiro da hankullan su wadanda ke a takaice, wanda bai san hakikanin wanda ake gudanar da dokar a kan shi ba, kuma ba tare da diba dukkan bangarori ba, sa'an nan ba tare da la'akari da dukkan abin da zai iya abkuwa ba".

Daga kuma ababen da suke karfafa abin da suka gabata akwai abin da muke gani a cikin rayuwar mu ta yau da kullun, wanda ke shi ne: bukatuwar namiji zuwa ga matar shi tare da cewa babu damar samun biyan bukatar, ko dai saboda rishin lafiyar matar, ko kuma saboda manyantar ta wajen shekaru, kuma tare da cewa suna son su ci gaba da rayuwa tare da juna. To kaka za su yi ?

 

A nan ma akwai zabi ukku:

 

1 – muce da shi namijin: a'a, doka ta hana ka yin wani aure, dan haka dole ka yi hakuri ka manta me ke mace a rayuwar ka, dan auran naka abu ne da ya sabawa son ran matar ka !

2 – muce da shi: ka je ka nemi mata ka abokance su, ka rika kuma samun damar biyan bukatar ka ta bangaren saduwa !

3 – mu ce da shi: ka je ka yi wani auran, ba tare da ka saki matar ka ta farko ba …

- Zabi na farko ya saba wa dabi'ar dan adam da bukatun shi, kuma ya saba wa abin da zai iya, dan haka za mu jefa shi cikin azaba a sauran rayuwar shi. Wannan kwa shi ne abin da muslunci ya magance.

- Zabi na biyu ya saba wa zabin muslunci wanda ke umarnin mu da kyawawan dabi'u, kamar yanda ya saba wa manufar muslunci na ganin cewa dan adam ya daukaka a cikin rayuwa mai tsabta da koncin hankali, kar kuma rayuwar shi ta kasance kamar rayuwar dabbobi.

- Zabi na ukku shi ne zai biya wa dan adam bukatun ran shi, wadanda Allah Ya halicce shi da su, kuma ya bar ita matar ta shi a matsayin matar aure, tana samun tausayawa daga mijinta.

Irin haka kuma yana faruwa yayin da matar zata kasance ba ta aifuwa, tare da cewa   mijin ta yana da bukatar samun diya. Dan haka zai samu kan shi gaban zabi biyu, babu na ukku:

1 – ya saketa dan ya auri wata mai aifuwa.

2 – ya auri wata amma tare da sakin ta farko.

"Za ta iya yuwa a samu wasu wadanda ma su son rai ne, maza da mata da za su ce: zabi na farko shi ne ya fi, yayin da za mu samu kishi tis'in da tara cikin dari za su fifita zabi na biyu, tare da yin Allah wadai ga wadanda suka fifita zabi na farko ! zabin da zai rosa masu gidajen su. Kuma ita wadda ba ta aifuwa za ta samu kore kewa da yaran matan nan ta biyu, kasancewar ita Allah bai bata aifuwa ba".

"Kuma zai iya yuwa ya kasance shi mijin nata mai bukatar yawaita aifuwa ne, ita kuma matar ta kasance ba mai yawan aifuwa ce ba, idan ya kara aure sai ya cinma manufar shi wacce ke kyakyawa; domin manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya yi umarni da ita kamar cikin fadar Shi: "ku auri mata wadanda akwai so tsakaninku, ma su yawan aifuwa; saboda ni ina neman yawaita al ummah ta da ku".

Kamar yanda a wasu lokutta za ka samu namiji yana da yawan balaguro, kuma zai iya daukar lokaci mai tsayi a cikin tafiyar shi, tare da cewa ba zai iya tafiya da matar shi ba; to, zai samu kan shi a cikin wannan halin tsakanin abubuwa guda biyu game da bukatar shi ta saduwa da mace:

1 – ko dai ya nemi wata mace da zai rika biyan bukatar shi ta haramtattar hanya.

2 – ko kuma ya auri mace ta biyu, aure na shari'a.

Babu shakka zabi na biyu shine abin zabi ga dukkan mai hankali, saboda zabi na farko akwai yada alfasha da fasadi da cututtuka a cikin shi.

Kamar yanda tsari na bada dama ga kara aure zai kawo gudun mawa wajen warware wasu matsaloli; daga ciki:

A – mace wacce mijin ta ya rasu ya bar mata diya, muslunci ya karfafa auran ta saboda ababe guda biyu: na farko: kare mutuncin ta da biya mata bukatun ta, domin kar ta fada cikin abin da zai tozartar da ita. Abu na biyu: kula da diyan ta, tare da tarbiyar su; domin manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya ce: "ni da wanda ya dau nauyin maraya tamkar wadannan ( yatsun ) biyu ne". Malik ya yi nuni ga: manuniyar shi da yatsar tsakiya.

B – mace wacce ba ta da kyaw, ko kuma tana da illa a gabben ta, shin za mu hana mata jin dadin zaman aure da arziki na diya, dan kwai bat a da kyau ? A'a, muslunci yana umurnin mu mu auri irin wadannan mata domin mu sanya farin ciki a cikin zukatan su.

C – mace da ta zauna lokaci mai tsawo ba tare ta samu aure ba, alhali kwa tana bukatar shi, tabbas wannan mata za ta fifita kasancewar ta matar wani mai wata matar a kan ta ci gaba da zama ba da miji ba.

Haka ne 'yan uwa idan muka tsaya muka diba al amurin da idon basira za mu ga cewa wannan hukunccin kamar sauran hukunce hukunce na muslunci sune magani ga matsaloli da dan adam yake fama da su; domin hukunce hukunce ne da suka zo daga ubanjin da Ya halicce su, wanda kuma Shi ne ya san kaka Ya halicce su, kuma menene yake tafiyar da rayuwar su, sabanin wadanda suke kokarin yaudarar mata da maganganu masu dadi a zahiri, wadanda a hakika babu inda za su kai su imba ga nadama da halaka ba.

Mun ga wasu daga cikin hikmomi na shar'an ta auran fiye da mace guda, tare da kayyade shi da adalci.

Allah madaukaki yana cewa: { ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu- biyu, da uku- uku, da huɗu- huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, ( ku auri ) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba } [ Suratul Al-Nisa 3 ].

Shar'anta wannan hukunci yana biyan bukatar dan adam da Allah ya sa masa a ainafin halittar shi, kuma rayuwa ta yau da kullun tana tabbatar da haka. Kamar yanda yake kare jama'a daga abkawa cikin rayuwar dabbobi, ta kara zube, wadda ba ta san menene mutun ci ba.

Abin lura a nan shi ne: idan wasu sun yi anfani da wannan damar, ba tare da cika sharadi ba, wajen cimma manufar su ta shahawa, da abkawa cikin kurakurai, to, lalle wannan ba abu ne da za' a dora wa muslunci ba; domin muslunci ba da haka ya yi umarni ba.

Da haka kuma za mu ga cewa dukkan abin da Allah ya hukunta, Ya hukunta shi ne da hikma, kuma dan maslaha ta bayin Shi, wannan kwa koda ba su gano wannan hikmar da wannan maslhar ba har zuwa wani lokaci, domin hankalin dan adam takaitacce ne, ba ya isa ga kome.

A karshe:

Gotav lobon yana cewa: "lalle tsarin auran fiye da mace guda tsari ne mai kyau, ya daukaka halayya ta gari a wajen ma su aiki da shi, kuma yana sanya 'yan uwa su kama juna, kuma yana baiwa mace girmanta da matsayi da jin dadi wanda ba zata same shi a Europe ba"

Shi kwa Bernard Sho cewa yake: "lalle Europe dole ne ta koma zuwa ga tsari na muslunci kafin karshen karni na ishrin, ta ki ko ta so".

Wata marubuciya kwa 'yar Britaniya cewa ta yi: "lalle 'yan mata wadanda suka shiga yawan banza sun yi yawa a wajen mu, kuma bala'i ya game kowa da kowa, kuma masu bincike sun kasa gano sababin hakan. Yayin da nike ganin wadannan 'yan matan a matsayina na mace, rai na yana bacewa dan tausayi da son da nake musu, amma bakin ciki na da me zai anfane su; ko da kwa dukkan mutane sun kasance kawa ta ? saboda babu abin da zai anfane su imba abin da zai magance matsalar su a aikace ba"

Ga kuma babban masanin nan da ake kira "Tos" yana mai dwora yatsar shi a kan cutar, kuma yana fadin menene zai magance ta, yayin da ya ce: maganin shi ne mu bai wa namiji damar auran fiye da mace guda, da haka ne kawai za mu magance wannan bala'i dan 'yan matan mu su kasance uwayen gida. Bala'i, dukkan bala'i yana cikin hana wa namiji a Europe auran fiye da mace guda; wannan hanin shi ya sa 'yan mata yawan banza, kuma ya jefa su cikin aikin maza, kuma dole ne sharri ya girma muddun dai ba mu baiwa namiji damar auran fiye da mace guda ba !

yawan adadin maza masu aure, wadanda ke da diyan da ba na aure ne ba, ya zama nauyi da wahala ga jama'a, inda an halitta aure fiye da guda da abin da wadannan mata da diyan su suke fama da shi na kaskanci da azaba, da bai auku ba, da kuma an kiyaye mutuncin su da na diyan su. Lalle gogayyar mata da maza zai kai mu ga halaka. Shi ba kwa ganin yanayin halittar ta yana cewa: abin da ke kanta ya sha banban da abin da ke kan namiji ? idan aka halitta Karin aure, to, lalle ko wace daya daga cikin su za ta kasance uwar gida da yara halittatu.

A karshen karshe: ya bayyana gare mu cewa bayan bijirar da wannan mas'ala ta auran fiye da mace guda a muslunci, girman hukunce hukuncen muslunci, kuma cewa: su hukunce hukunccen nan masu girmama mace ne su kai ta ga tsololuwar daraja; domin muslunci Ya zo da shari'a mai adalci, wacce tayi daidai da ko wane zamani, kuma ta dace da ko wane guri, da ko wane mutun.

Shari'ar muslunci tare da kamalar ta, da rahamar ta, da saukin ta, tana sanya dan adam cikin dadin kai na rayuwa a ko wane lokaci, a duk inda yake, tana sanya shi ya rayu rayuwa mai dadi, cikin nutsuwa; wannan kwa dan ta zo ne daga Allah, masanin kome, mai sanya kome a inda ya dace, mai kuma tausayin bayin Shi.

 

Ma rubuci : mut'ab al- harisi