Musuluncin salman- al farisi ( Allah Ya kara yarda da shi )


Da sunan Allah mai rahama, mai jin kai

 

Musuluncin salman- al farisi ( Allah Ya kara yarda da shi )

 

Yana daga cikin kissosi masu ban mamaki yanda salman- al farisi ( Allah Ya kara yarda da shi ) ya shiga cikin addinin muslunci.

ga kuma kissar kamar yanda shi da kan shi ya ruwaito ta, yana mai cewa: » na kasance bafarise, mutunen kauyen "Jah" dake yankin Asbahane, ma'aifina kwa ya kasance mutunen "dahkane", kuma na kasance mutun mafi soyuwa agare shi. Dan tsananin son da yake mini ya daure ni a cikin gida kamar yanda ake tsare yarinya.

 

na bada kwokari mutuka cikin addinin majusanci, har ma na kasance mai kula da hura wutar da ake bautawa, wacce kuma ba' a bari ta mutu !

Ma' aifina ya mallaki dukiya mai yawan gaske, wata rana ya shagalta a cikin wani gida na shi, sai yace da ni: ya da' na, yau na shagaltu, ka je  dan ka kula da dukiya ta.

A hanya ta na isko wani wurin bauta na nasara ( coci ), sai na ji muryoyin su yayin da suke salla, kuma na kasance ban san menene sababin da ya sanya mutane suka baiwa ma' aifina shawarar ya tsare ni a cikin gida kar ya barni na futa; yayin da na wuce ta wajen su ina mai jin muryoyin su, sai na shiga domin na ga me suke aikatawa.

Da na shiga sai al amarin su ya kayatar da ni mutuka, musamman sallar su, sai na ce: wallahi wannan ya fi addinin da muke a kai; wallahi ban rabu da su ba har sai da rana ta fadi, ina mai barin dukiyar baba na.

Sai nace da su: ina ne asalin wannan addini ? sai suka ce da ni: kasar sham. Sa' annan na komo wajen baba na bayan kwa ya aika wajen nema na, kuma na shagaltar da shi daga ayukkan shi.

Yayin da na dawo sai ya ce: da na, ina ka tafi ? shin ban aike ka ba ? sai na ce: ya baba na, na biyo wajen wasu ne, suna salla a cikin wata coci, sai abin da na gani na addinin su ya birgeni, shi ya sa wallahi ban rabu da su ba sai da rana ta fadi.

Sai baba na ya ce: wannan addinin ba bu alkhairi cikin shi, addinin ku na iyaye da kakanni ya fi shi. Sai na ce: a' a, wallahi wannan ya fi addinin mu, sai ya ji tsoron kar in canza addini, sai ya sanya mini mari, ya tsare ni a gida.

 

Sai na aika wajen nasarawa ina mai cewa: idan 'yan kasuwan nasarawa suka zo daga kasar Sham, ku bani labari. Yayin da suka zo sai suka bani labarin cewa akwai wata tawaga ta zo, sai na ce da su: idan suka biya bukatar su, kuma suka yi niyar komawa gida ku gaya mini.

Da suka so komawa gida sai suka gaya mini, ni kuma na hudda wannan marin daga kafafuwa na, na guda ina mai bin su har zuwa Sham. Da muka isa, sai na ce: wanene fiyayyen mutun a cikin wannan addini ? sai suka ce da ni: malami da ke cikin coci. Sai na je wajen shi, na ce da shi: ina son shiga wannan addinin, kuma ina son kasancewa tare da kai, ina mai maka hidima, ina kuma mai karatu wajen ka, da salla tare da kai. Sai ya ce: ka shigo, sai na shiga wajen shi. ya kasance mutun mai sharri da rishin kirki, yana umarnin mabiyan shi da su kawo sadaka kuma yana kwadaitar da su akan ta, idan suka tara wannan sadakar sai ya rike ta ba ya rabawa miskinai ita, har sai da ya tara dukiya mai yawa; sai na tsane shi tsana mai yawa; saboda abin da na gani a tare da shi na rishin kirki.

 

Bayan ya mutu nasara sun taru dan bunne shi, sai na ce da su: wannan ba mutunnen kirki ne ba, yana umarnin ku da ku yi sadaka, idan kun tara dukiyar sai ya ajiye wa kan shi ita, ba ya rabawa miskinai komi daga ciki, sai suka ce: yaya aka yi ka san da haka ? sai na ce: ni zan gwada muku taskar shi, da muka je wajen ta sai suka same ta dukiya mai yawan gaske da ta kunshi zinariya da azurfa. Da suka ga wannan dukiya sai suka ce: wallahi ba za mu binne shi ba har abada. Suka tsire shi, suka kuma jefe shi da duwatsu, tare da sanya wani mutun a bagiren shi, wanda banga kamar shi ba; mai zuhudu, mai kaunar lahira, mai korarin ibada safiya da dare; sai na so shi, so mai yawan gaske.

Na kasane tare da shi wani lokaci, yayin da mutuwa ta zo mashi sai na ce da shi: na kasance tare da kai, kuma ina matukar son ka, kuma ga ka a halin rabuwa da duniya, wajen wa za ka mani wasiyar in kasance tare da shi ? sai ya ce: da na, wallahi ban san wani – a yau – da ke ka abin da nake akai ba, dukkan mutane sun halaka sai wani mutun guda a garin "Mausil", sunan shi wane, shi ya na kan abin da ni ke a kai, ka je wajen shi.

Bayan ya mutu , kuma aka binne shi, sai na tafi garin "mausil"  wajen mutunen da ya gaya mani, na ce da shi: wane, wane ne ya mani wasiya na zo wajen ka bayan mutuwar shi, kuma ya ce: kai kana kan abin da yake a kai. Sai ya ce da ni: ka zamna tare da ni, da na zamna tare da shi na same shi mutunen kirki kamar wanda ya gabace shi, yayin mutuwa ta zo mashi, sai na ce da shi: wane, lalle wane ya mani wasiyar zuwa wajen ka, kai kuma wajen wa zaka umarce ni na kasance bayan ka ? sai ya ce : da na, wallahi ban san wani da ke kan abin da muke kai ba, sai dai wani mutun guda a garin "nasibin", shine wane, ka je wajen shi.

 

Da ya rasu, aka kuma binne shi, sai na je wajen wancan na "nasibin" na kuma bashi labarin kissa ta, sai ya ce: ka zamna waje na, na kuma same shi kamar wadanda suka gabace shi, ba mu jima tare ba yayin da mutuwa ta zo mashi, sai na ce da shi: wane, lalle wane ya mani wasiya na je wajen wane, shi kuma ya mani wasiya na zo wajen ka, kai kuma zuwa wajen wa zaka mani wasiya ? sai ya ce da ni: da na, wallahi ban san wani da ke kan abin da muke kai ba banda wani mutun a garin "ammuriyah" idan kana so ka je wajen shi, lalle shi yana kan abin da muke kai.

Bayan ya mutu kuma aka binne shi, sai na je wajen mutunnen "ammuriyah", na ba shi labarin al amari na, na zamna tare da shi, kuma na same shi kamar yanda wadanda suka gabace shi suka kasance, kuma na tara dukiya har na samu shanu da tumaki, sa' annan mutuwa ta zo ma shi, sai na ce da shi: wane, wajen wa zaka mani wasiya na tafi ? sai ya ce: wallahi, ban san wani mutun da ya yi saura a kan abin da muke akai ba, wanda zan umarce ka kaje wajen shi, amma ka shigo zamanin wani annabi, Shi abin aikowa ne da addinin Ibrahim (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ); zai huto a kasar larabawa ne (a cikin wata riwaya: za' a aiko shi ne a kasa mai tsarki ), zai yi hijira zuwa wata kasa da ke tsakanin kwonannun duwatsu guda biyu, tsakanin su akwai itacan dabino da yawa, akwai alamomi bayyannanu a tare da shi: yana cin abin da ke kyauta ne amma ba ya cin sadaka, akan kafadar Shi akwai tambarin annabci, idan za ka iya zuwa wajen shi ka tafi.

Bayan ya mutu kuma aka binne shi, na zauna a "ammuriyah" wani lokaci da Allah Ya kaddara, yayin da wasu larabawa 'yan kasuwa daga kabilar kalb suka zo, sai na ce da su: za ku iya dauka ta zuwa kasar larabawa na baku shanu da tumaki da na mallaka ? sai suka ce: mun yarda.

Sai na ba su dabbobin kuma suka tafi da ni, yayin da muka iso wadil kura – kworama ce tsakanin garin Madina da kasar Sham wanda wajen shi akwai garuruwa da yawa - da muka zo nan sai suka zalunce ni, suka saida ni ga wani bayahude.

Na kasance wajen shi, da na cewa a wajen akwai itacen dabino da yawa, sai na yi fatan kasancewar nan ne aka sifanta mani. Ana cikin haka sai wani dan kawun shi daga bani kuraiza ya zo wajen shi daga Madina, sai ya sayar da ni gare shi, sai ya dauke ni zuwa Madina, wallahi tunda muka isa cikin ta sai na ganta kamar yanda malamin nan ya sifanta mani.

 

na zamna cikin ta har Allah Ya aiko annabin shi, Ya zamna a Makkah tsawon wani lokaci da Allah Ya kaddara, ba na jin labarin Shi, domin na shagalta da ayukkan bauta. Sa' annan sai Ya yi hijira, wallahi ina saman itacen dabino na mai gida na, shi kwa yana kasa yayin da wani dan kawun shi ya zo wajen shi, ya ce da shi: wane, Allah kar Ya albarkanci Annabin larabawan Madina (Aus da Khazraj ), wallahi yanzu sun hadu a Kuba'a wajen wani mutun da ya zo daga Makkah, wanda suke da'awar annabi ne.

 

Yayin da na ji haka sai makarkata ta kama ni har na yi tsammanin fadowa zan yi daga kan uwar dabinon nan akan mai gida na, sai na rika cewa wannan dan kawun mai gidan nau: me ka ke cewa ? me ka ke cewa ? sai mai gida na ya ji haushi, ya shure ni da kafar shi, sa' annan ya ce: menene ya dame ka da wannan ?  ka ci gaba da aikin ka, sai na ce: ba kome, kawai na so in tabbatar da wannan zancan ne.

Na tara wani abu na daga dukiya, sai na tafi da ita zuwa ga manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) da yamma, na same Shi a Kuba'a, na shiga wajen Shi, na ce da Shi: na samu labarin cewa kai mutunen kwarai ne, kuma akwai mutane mabukata cikin abokanan ka; wannan wata sadaka ce wacce naga ku ne kuka fi cancantar a baku ita, sai na kusantar da ita zuwa gare Shi, sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya ce wa sahabban Shi: ku ci, Shi kuma Ya kame bai ci ba, sai na ce a rai na: daya kenan.

Sai na tafi kuma na tara wani abu na dukiya - Shi kwamanzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya shigo Madina - sai na zo na ce da shi: naga ba ka cin sadaka, to wannan kyauta ce wacce na kawo maka, sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya ci daga cikin ta Shi da sahabban shi, sai na ce a zutiya ta: biyu kenan.

Sa' annan na zowa manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) a baki'a ya rako gawa, yana zaune, sai ya ga ina kokarin diba wani abu a bayan Shi, bayan na mashi sallama, da ya ga haka sai ya dage mayafin da ke kafadar Shi, da na ga wannan tambari sai na fada kan Shi ina mai kuka; sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya ce da ni: kau daga nan, sai na kau, sai kuma na gaya mashi kissa ta tun farko kamar yanda na gaya maka ya kai dan Abbas, sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya so sahabban Shi su ji kissata.

 

Bayan haka sai bauta ta shagaltar da Salman; abin da ya zama sanadiyar rasa "Badar" na farko.

Sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya ce da ni: ya salman, ka yi yarjejeniya ta 'yanta kanka, sai muka yi yarjejeniya akan na dasa masa itacen dabino guda dari uku, na kuma bashi ukiya arba'in.

Sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya ce da sahabban Shi: ku taimaka wa dan uwan ku, sai suka hada mani uwar itacciyar dabino dari uku; akwai mai kawo talitin, akwai mai kawo ishrin …

Sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya ce mani: ya kai Salman, ka je ka yi gina, bayan haka sai ka kiraye ni dan na dasa su da hannaye na, yayin da na gama gina rami sai na kirawo shi,  sai Ya zo tare da ni, sai mu ka kasance muna kusanto ma Shi uwar itacen nan, Shi kwa yana dasa su, sai ya kasance dukiyar kawai ita ta yi saura a kai na; sai aka zowa manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) da kwatankwacin kwan kaza na zinariya daga wani yakin jihadi, sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) ya ce: ina mutunen nan na farisa da ya yi yarjajjeniya da mai gidan shi ?

Ya ce: sai aka kiraye ni na zo wajen Shi, sai Ya ce da ni: ya salman, ka dauki wannan ka je ka biya, sai na ce: ya manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ), yaya za ayi wannan ya isa ? sai manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) Ya ce da ni: dauki, Allah zai biya maka bashinka da wannan.

 

Ya ce: sai na dauke wannan dukiya, na auna masu daga ciki ukiya arba'in, na rantse da wanda rayuwar salmana ke Hannun Shi, sai na biya hakin shi, kuma na samu 'yanci kai, aka 'yantar da ni, sai na kasance tare da manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi ) a yakin ahza'b, bayan haka wani yaki bai sake kubce mani ba« .

] Imam Ahmad ne Ya ruwaito wannan hadisi a cikin "musnad (5/441-444) kuma Shu'aibul Arna' utt da husainil Asa'd a cikin aikin da ya yi wa siyaru  a' alamun nubala'a (1/511) sun ce: sanadin wannan hadisi mazajen Shi dukkan su adilai ne, kenan wannan sanadi mai karfi ne[ .