tsinkayen nesa a wajen Khadija 'yar Khuwailid


    Al ummar laraba al umma ce mai alfahari da mai hali nagari; ko mai gaskiya, ko mai karamci, ko mai jarumta, ko mai hikima, ko Mai jin ƙai,ko mai kare kai

daga alfasha, ko kuma mai sada zumunta... a wajen su yana samun ɗaukaka da matsayi da girmamawa a cikin su. Wannan kwa shine matsayin da khadija 'yar khuwailid takeda a cikin su, domin ta kasance mai babban asali, da kuma kyawo tshakanin matan Makkah. Ta samu labarin amanar manzon Allah (tshira da amincin Allah su karu a gareShi), da gaskiyarSa, da kyawawon halayyarSa; dan haka ta aika zuwa gare Shi, tana mai bujuro maSa aiki cikin fataucin ta zuwa Sham. Sai Ya amince, Ya kuma futa da dukiyar ta zuwa can Sham, kuma ya kasance tare da Shi a cikin wannan tafiyar akwai yaron ta da ake kira Maisara.

 

Maisara ya ga cikin siffofin Muhammad (tshira da amincin Allah su karu a gareShi): hikma, da cikar hankali, da kyawawan halaye, da iya gudanar da al amurra cikin wannan fatauci; dan haka sai ya samu nutshuwa da koncin hankali game da Mohammad (tshira da amincin Allah su karu a gareShi).

 

kuma abin da ya ƙãra bashi mamaki da sha'awa shine abin da ya gani na lura ta musamman da malamin kirista Nistor ya baiwa Mohammad lokacin da su ka zo, suna hutawa kusa da cocin sa, kuma labarartar da shi Maisara da ya yi cewa: yana ga alamomin annabta da annabi Isa Ya fada a cikin linjila.

 

Bayan dawowarsu daga Sham sai Maisara ya baiwa Khadija labarin abin da ya gani tare da Muhammad a cikin wannan tafiya; ababen da ya gani game da halayen Sa, da dabi'unSa na gari, kuma ya bata labarin kissarSa tare da Nastur; sai Khadija ta kara al'ajabta da Mahammad, kuma ta ga cewa Shine mutunan da ya cancanta ta aura. Kadija kwa ta kasance zawara da dukkan mayan mutane ma su daraja a Makkah ke begen aure. Sai ta tura abokiyarta zuwa ga Muhammad domin ta bijiro maSa da maganar aure, kuma ta tambaye Shi: me yake hana ka aure? Sai Ya ce: ba ni da halin aure. Sai ta ce da Shi: idan aka dauke maka nauyin abin aure, kuma aka bijoro maKa mace mai kyau da daukaka zaKa yarda? Sai Ya ce: wacece? Sai tace: Khadija, sai Ya yarda, kuma Ya tafi tare da kawun Sa domin neman auren ta, sa'annan aka yi auren nan mai albarka, kuma ta kasance fiyayyar mace ga mijin ta. Da ita ne Kwa aka arzuta Shi dukkan 'ya'yan Sa - ban da Ibrahim -: Alkasim, da zainab, da Rukayya, da Ummu Kaltum, da Fatima. 

 

Sai Muhammad ya kasance Yana son kebanta; kuma Ya kasance yana kebanta a dũtsen Jabalan Nur a kogon Hira. Anan Mala'ika Jibril (alaihis salam) ya zo maSa, Yace da Shi: I karatu, sai Ya ce da Shi: ban iya karatu ba, sai Jibril Ya matse Shi sosai, sa'annan Ya sake Shi, kuma ya maimaita hakan har sau uku, sa'annan Jibril Ya ce da Shi: {karanta da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta (1) Ya halicci mutun daga gudan jini (2) Karanta kuma Ubangijinka ne Mafi karimci}. sai Muhammad Ya komo wajen Khadija a tsorace, Yana mai cewa: ku lullube Ni, sai Khadija ta lullube Shi har lokacin da tsoro ya sake Shi, sa'annan Ya gayama Kadija kissar Sa, Ya kuma ce da ita: ina ji ma kai na tsoro.

 

A nan kwa kaifin hankali da hikma da basirar ta sun bayyana, duk tare da cewa tana tsoro abin da ya gani ya kasance aikin shaidanai da aljannu ne, ta ce da shi a cikin natsuwa: Allah ba zai taba tozartar da kai ba; domin Kana sadar da zumunta, kana daukar nauyin magajiyi da maraya, kuma kana taimakawa maras akwai, kuma kana karramar da bako, kuma kana taimakawa a cikin ayukkan alkhairi.

 

Ka diba yadda ta yi aiki da hankali, da kuma tunaninta game da sakamako da zai iya kasancewa ga wanda ya hada wadannan dabi'u kyawawa: (Allah ba zai taba tozartar da kai ba); domin wannan dabi'u ba za su hadu a tare da mutun ba, kuma Allah Ya tozartar da shi.

 

Wannan al'amari kwa ya kasance shahararre ne a cikin Larabawa: cewa wanda aka sani da gaskiya, da karamci, da kame kai, da kyawawan dabi'u; suna masa zaton kyakyawon karshe, da matsayi mai girma da daukaka, tare da karbuwa wajen jama'a.

 

Wadannan halaye suna daga cikin dalilai na hankali masu karfi da Khadija ta yi anfani da su wajen sanin gaskiyar abin da mai gidan ta Muhammad Ya gani kuma Ya labarar da ita. Amma duk da haka ta hada da dalili na abin da ya zo a cikin litattafai da suka zo daga Ubangiji da ke tabbatar da hakan; sai ta hada dalilai na hankali da dalilai wadanda suka zo a cikin litattafai.

 

Don haka sai ta tafi da Shi zuwa ga dan baffan ta warƙah ibn Naufal, wanda ya kasance yana da ilimi na addinai da suka gabata, ya kasance ya manyanta kuma

   ya makauce. Sai Khadija tace da shi: ya dan baffa na, ka saurari dan dan uwan ka! Sai warƙah yace da Shi: ya dan dan uwa na, me kake gani? Sai manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) Ya fada masa abin da Ya gani, sai Warƙah ya ce da Shi: wannan Shi ne abinda ya sauka wa Musa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi)! Da ma a ce ina matashi rayayye lokacin da mutanen ka za su fitar da kai (daga garin Makkah), sai Ya ce: kenan za su fitar da ni? Sai ya ce: ƙwarai kwa; ba wanda ya zo da irin abinda ka zo da shi face an masa adawa, idan lokacin ya sameni a raye zan taimaka maKa da dukkan karfi na.

 

Dalili na hankali dake tare da Khadija ya hadu da dalili na littafanda suka gabata wanda Warƙah ya sanarda su; dan haka sai Khadija ta tabbatar da cewa Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) annabi ne, manzo ne daga Allah ; dan haka ta kasance mutun na farko da ya yi imani da Shi.

 

Amma a wajen Warƙah dalili na litattafan addinan da suka gabata sune abin dogaro wajen tabbatar da manzancin Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi); domin sifofin sun zo a cikin At taura da Linjila, tare da cewa Shine annabi na karshen zamani wanda zai futo daga zurriyar annabi Isma'il, wanda zai futo tsakanin duwatsun Makkah, kuma mala'ikan da Ya gani Shine mala'ikan da Ya zo annabawa da suka gabata.

 

Khadija (Allah kara yarda da ita) ta rayu rayuwa mai girma tare da manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi); kuma ta kasance mai bada gudun mawa ta musamman wajen isar da da'awa ta manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi); duk a lokacin da aka cutar da Shi tana karfafa Shi, tare da kawar maSa dukkan wata damuwa.

 

Khadija (Allah kara yarda da ita) ta rayu da manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) cikin wahalhalu, tana mai hakuri, mai neman lada wajen Ubangiji har Allah Ya karbi rayuwarta tanada fiye da shekaru sittin, kuma manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) da kan Shi ya shiga rami domin bunne gawarta.

 

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) Ya rayu Yana mai rike alkawali game da Khadija, Yana mai yawaita yabon ta, Yana sadar da abokananta da kyaututtuka, abinda ma ya sa Aisha (Allah kara yarda da ita) ta nuna kishinta; kamar yanda ya zo a cikin "sahihil Bukhari" tana cewa: "ban yi kishi da daya daga matan manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) kamar yanda na yi kishi da Khadija alhali ban taba ganinta ba; amma manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) Yana yawan anbaton ta, wani lokaci ma zai yanka rago, Ya gungunta shi, Ya rarrabawa abokanan Khadija; sai na ce da Shi watarana: kamar ba wata mata a duniya bayan Khadija! Sai Ya ce: Ita ta kasance... kuma ta kasance.. kuma ina da "ya'ya daga gareta".

 

Khadija ta samu falala mai girma sakamakon gaskiyar ta, da kuma taimaka wa manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi). A cikin "sahih muslim" an karbo daga Abu Huraira, yana cewa: "Jibril (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi) Ya zo wajen manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi), sai Ya ce: ya manzon Allah, ga Khadija nan za ta zo, tana da kwano wanda a cikinsa a kwai miya, ko abinci, ko abin sha, idan ta zo, Ka isar da sallamar Ubangijinta zuwa gare ta, kuma Ka isar da sallamata kazalika, sa'annan ka yi mata albishir da wani gida a cikin Aljanna, gida wanda babu hayaniya ko wahala a cikin sa".

 

Hakika wannan tarihi ne mai mutukar kyau da kayatarwa, tare da kodaitarwa da Aljanna, kuma yana nuna mana dogon tunanin wannan mata da hangen nesan ta, wanda a sakamakon haka ne Allah Ya aika mata da gaisuwa, kuma Jibril ma Ya mata sallama!! Allah kara yarda da ita.

 

Marubuti: mut'abul harisi